Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, Abdullahi Adamu, ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar.
BBC ta rawaito cewa, Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.
- Adamu Yana Ganawar Sirri Da Sanatocin Da Za Su Yi Wa Jam’iyyar APC Takara
- Sanatocin APC 3 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP da NNPP
Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.
Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar Edo.
Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Adamu ya ce akwai takaici irin yadda ‘yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.
” Ban damu da abinda ke faruwa a wata jam’iyya ba, damuwa ta itace abinda ke faruwa a jam’iyyata.”
” Babu Shugaba nagari da ba zai damu ba idan ya rasa mamba ko da daya ne a jam’iyyarsa, ballantana a yi maganar mamba biyu, ko uku.”, in ji Adamu.
Sai dai Shugaban APCn yace suna kan tattauna hanyar da zasu dinke wannan baraka ta ficewa daga jam’iyyar, duk da ya ce ba wani sabon abu bane.