A shekarar nan ta 2023 ne ake cika shekaru 10, da gabatar da shawarar nan ta kafa al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ga al’ummun kasa da kasa.
Yau 4 ga watan Afirilu, cibiyar nazarin hada hadar kudade ta Chongyang, wadda ke karkashin jami’ar Renmin ta kasar Sin, ta fitar da wani muhimmin rahoto, wanda ya zama karon farko da kwararrun kasar na gida da na ketare suka hadu domin nazartar ci gaban da shawarar ta haifar, cikin shekaru 10 da suka wuce.
Rahoton ya nuna cewa, shawarar samar da al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, wani sabon mataki ne na tabbatar da nasarar wanzuwar salo daban daban na wayewar kan bil Adama, kana wani sabon mataki ne na gudanar da harkokin duniya, kuma sabon salon musaya tsakanin sassan kasa da kasa. Har ila yau, hakan sabon tsari ne na hadin gwiwar shiyyoyi, kana sabuwar gudummawa ce da kasar Sin ta samar. (Saminu Alhassan)