Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta zargi daya daga cikin manyan ‘yan takarar jam’iyyar adawa, Peter Obi da cin amanar kasa, makonni kadan bayan da dan takarar jam’iyyar mai mulki ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana zargin a yayin ganawa da manema labarai a birnin Washington DC na kasar Amurka a ranar Talata.
Mohammed ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, da yunkurin tada hankalin jama’a kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, yana mai cewa, irin wannan ikirarin cin amanar kasa ne.
“Obi da mataimakinsa, Datti-Ahmed bai dace su dinga yi wa ‘yan Nijeriya barazanar cewa ba, idan aka rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC a ranar 29 ga Mayu, karshen mulkin dimokuradiyya a Nijeriya ya shude.
“Wannan cin amanar kasa ne. Ba zai yiwu su dinga zama suna gayyatar tayar da hankali ba, kuma abin da suke yi ke nan.” Inji Lai Mohammed