A yau Laraba 5 ga wata ne hadaddiyar kungiyar jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kididdiga game da farashin kayayyakin masana’antun kasar a watan Maris da ya gabata.
Alkaluman sun nuna cewa, CPI na kasar ya ci gaba da karuwa a watan Maris, inda ya kai matsayin koli a cikin watanni 32 da suka gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasuwar kayayyakin masana’antun kasar Sin tana gudana yadda ya kamata.
Rahotannin sun nuna cewa, CPI na kasar Sin a watan Maris ya kai kaso 103.4 bisa dari, wato ya karu da kaso 0.6 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Fabrairu, inda ya kai matsayin koli tun bayan watan Agustan shekarar 2020. Lamarin da ya nuna cewa, kasuwar sayayya za ta kara habaka a kasar, sakamakon farfadowar tattalin arzikin cikin gida da sana’ar kire-kire, da kuma karuwar bukatun kasuwar kasar. (Mai fassarawa: Jamila)