Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Kashim Shettima ya yi alkawarin dakatar da kwace da markade babura a babban birnin tarayya Abuja da sauran sassan Nijeriya idan suka fara mulki.
Shettima wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da kungiyar masu babura da babur mai kafa Uku (Keke-napep) ta kasa a Abuja, ya roki ‘ya’yan kungiyar da su cigaba da kasance wa ‘yan kasa nagari masu bin doka da oda, domin gwamnati mai jiran gado, ta shirya tsaf don inganta rayuwarsu.
Zababben mataimakin shugaban kasar wanda ya ce babu wani nauyi da shugabanni ke dauka wanda ya wuce na amana, ya ce wannan kungiyar ita ma wakiliyar jama’a ce don haka ina tabbatar muku da cewa gwamnati mai zuwa za ta yi duk abin da ya kamata.