Nijeriya ta samu tallafin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya domin bunkasa shirinta na inganta rayuwar al’ummar kasar nan gabanin cire tallafin man fetur a watan Yunin wannan shekara, daidai lokacin da tattalin arziki ke tafiyar hawainiya.
Gwamnati ta ce za a raba tallafin ne ta hanyar amfani da na’urar aika kudi ga ‘yan Nijeriya kusan miliyan 50 ko gidaje miliyan 10, inda ta ce wadannan mutane suna cikin mafi raunin rukunin al’umma.
- Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasashen Yamma Kan Goyon Bayan Kungiyar Ta’addanci A NijeriyaÂ
- Shettima Ya Yi Alkawarin Kawo Karshe Kwace Da Markade Babura A Abuja
Ta ce hakan na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur a kan al’umma.
Bankin Duniya ya damu a kan cewa karuwar tattalin arzikin da Nijeriya ta samu na kashi 2.8, bai wadatar ba wajen rage tasirin fiye da kashi 40 na al’ummar da ke fama da matsanancin talauci.
Nijeriya da ta kasance kasa mafi girman tattalin arzikin a Nahiyar Afirka, ta ware Naira tiriliyan 3.36 a bana domin kashewa a matsayin tallafin man fetur har zuwa tsakiyar 2023 lokacin da za ta daina biya.
Nijeriya, ita ce kasa mafi yawan arzikin danyen mai a Afirka amma tana shigo da man fetur daga kasashen waje saboda rashin aiki da matatunta na mai ke yi.