Kafin mu zo kan batun Ittikafi, za mu karasa bayani a kan karya azumi da muka dauko yi a makon da ya gabata a shafi na 24.
Idan mutum ya san cewa bayan kowane kwana uku ga misali zai yi rashin lafiya, ko kuwa mace ta saba da haila ta zo mata ranar bakwai ga ko wanne wata, to, da ranakunnan suka zo sai suka ki daukar azumi suna jiran faruwar wadannan uzurai.
Za su yi ramuwa game da kaffara ko da kuwa rashin lafiyan ko hailar sun auku. Yadda shari’a ta ce su yi shi ne su dauki azumin, a locin da dalilin karya shi ya zo, suka gan shi zahiri sai su karya.
Makaruhi ne mutum ya dandani abinci dan ya ji ko maggi ko gishiri ya yi sosai a cikin abinci ko miya. Idan ya yi sauri ya tufar azumi bai baci ba. Idan kuwa ya hadiye azumi ya baci zai yi ramuwa da kaffara.
Haka kuma makaruhi ne mutum ya tattauna abinci a cikin baki saboda kananan yara, idan ya zubar da tukan ko kufan gishirin nan ko na abincin nan azumi bai baci ba. Idan kuwa ya hadiye shi da mantuwa ko bisa ga rinjaye zai rama daya, idan kuwa da gangan ne zai yi ramuwa game da kaffara. Haka kuma wanda ya lika magani a cikin kogon hakorinsa idan bai hadiye maganin ba azumi bai karye ba.
Idan mutum mai janaba ko mace mai haila da daddare ba su samu damar yin wanka ba sai da rana, azumi yana nan. Haka kuma idan mutum ya aikata sabon Allah da daddare, komai girman zunubin nan, wajibi ne washegari ya tashi da azumi, domin zunubin sabo daban ladar yin azumi kuma daban.
Sunnah ne mutum ya kame bakinsa daga dukkanin maganganun alfasha a cikin watan Ramadana kuma ana so ya yawaita ibada ga Ubangiji Allah. Kamar yin sallar asham da karatun alkur’ani da zikiri da tasbihi da zuwa wajen tafsiri.
Dukkan azumin da mutum ya karya da mantuwa ko bisa ga rinjaye, to, ba zai kara cin komai da gangan ba har rana ta fadi don alfarmar watan Ramadan, ko da yake zai rama azumin nan.
Idan kuma ya sake cin wani abu da gangan, bayan wannan na mantuwa to zai yi ramuwa game da kaffara.
Sunnah ne mai azumi ya gaggauta yin bude baki bayan ya tabbata lalle rana ta fadi. An so ya yi bude baki tun gabanin yin sallar magariba. Kuma sunnah ne ga mai yin azumi ya jinkirta sahur gwargwadon lokacin da zai isa ya karanci ayar Alkur’ani hamsin bayan kammala yin sahur kafin alfijir ya fito.
Sunnah ne ga mutum wanda ba mai hajji ba ya yi azumi ranar tara ga zulhajji, haka kuma mustahabbi ne mutum ya yi azumi cikin kwana tara na farko ga watan zulhajji.
Sunnah ne kuma ya yi azumi a rana na tara da ran goma ga muharram, da sauran kwanakin muharram, da watan rajab dana sha’aban, da kwana uku a cikin kowane wata, da kwana shida a cikin shawwal. Ana kiran wadannan da azumin Tadawwu’i, wato na sa kai.
Sunnah ne mutum ya gaggauta ramuwar azumin ramadana da ya sha. Amma Ya hallata a gare shi ya jinkirta ramuwa amma kuma dole zai rama kafin wani azumin watan ramadana ya zo. Idan kuma jinkirinsa ya yi muni har ya tsallake ramadana na gaba to zai yi sadaka da mudu daya a kowane maraice da ya rama dayan azuminsa.
Bayani A Kan Ittikafi
Ittikafi shi ne musulmi ya zauna a cikin masallaci domin yin zikiri da tasbihi da sallah da karatun Alkur’ani, yana mai yin azumi, mai kamewa daga yin jima’i da magabatan jima’i, har kwana daya ko abin da ya fi haka da niyyar yin ittikafi.
Hukuncin ittikafi sunnah ne mai lada da yawa, wajibi ne ittikafi ya zamo a cikin masallaci, mai yin sa kuma ya zamo yana mai yin azumi ko da farilla ko na tadawwi’i, kuma da sharadin kwanakin yin sa su jeru ba a yanke ba. A kallan kwanakin ittikafi kwana daya, mafi yawansa kuma kwana goma, a wani kauli kuwa an ce a kallansa kwana goma mafi yawansa wata daya.
Idan mutum zai fara kwanakin ittikafi da ya dauki alkawarin yi, zai shiga masallaci gabannin faduwar rana. Idan kuma ya kammala zai bar masallaci zuwa gida bayan magariba. Wajibi ne mutum ya cika adadin kwanakin da ya dauki alkawarin yi. Bai halatta ya rage su ba ta kowanne hali.
Mai ittikafi ba wai ba zai fita wajen masallaci ba sai domin larurar Dan’adam. Kamar tafiya cin abinci, da zuwa fitsari ko bayan gida ko wanka ko alwala. Kuma idan ya fita domin dayan wadannan abubuwa ba zai shige wuri mafi kusa da inda zai iya biyan bukatarsa ba. Idan ya je wuri mafi nisa ittikafi ya baci, sai ya faro tun daga farko. Amma idan rashin lafiya ya kama mutum, ko kuma jinin haila ko na biki ya zo wa mace, lokacin da suke yin ittikafi, to, za su fita su koma gida domin dayan wadannan uzurori. Amma da gushewar uzurinsu sai su dawo masallaci maza-maza su cigaba da ittikafinsu. Wato za su yi lissafi da kwanakin baya.
Kuma a lokacin zamansu a gida da uzuri, duk suna cikin hakkin ittikafi na barin yin jima’i da makamantansu.
Idan mai ittikafi ya ci abinci da rana da gangan ko ya yi jima’i da rana ko da daddare da gangan ko da mantuwa ittikafi ya baci, sai ya faro shi tun daga farko.
Mai ittikafi ba zai fita masallaci don gaida marasa lafiya ba, sai idan dayan iyayensa ne. Kuma ba zai fita don sallah a kan mamaci ba, ko don yin ciniki ba.
Idan karshen kwanakin ittikafin mutum ya dace da daren sallah, to, ana so ya dakata har zuwa washegari, daga nan masallaci ya zarce zuwa masallacin idi, sannan daga nan ya taho gida.