Jam’iyyar APC a Jihar Gombe ta dakatar da Sanata Amos Bulus bisa zargin yi mata zagon kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Moses Kyari, sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, ya sanyawa hannu ranar Asabar a Gombe.
- Gwamnatin Kaduna Ta Dage Dokar Hana Fita A Chikun
- Jami’ar MAAUN Kano Ta Rantsar Da Dalibai 1,200 A Zangon Karatu Na 2022/23
Kyari ya ce jam’iyyar ta kuma dakatar da dan majalisar wakilai Yunusa Abubakar mai wakiltar mazabar Yamaltu-Deba a majalisar dokokin tarayya bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Ya ce shugabannin unguwanninsu sun dakatar da ’yan majalisar ne bayan an same su da aikata laifukan cin hanci da rashawa a lokacin zaben 2023 a jihar.
Kyari, ya ce shugabannin Unguwar Bambam da ke karamar hukumar Balanga ne suka dakatar da Sanatan.
“An dakatar da shi (Bulus) ne saboda yakar jam’iyya a babban zaben da aka kammala.
“Hakan ya faru ne sakamakon wata takardar koke da aka rubuta daga unguwarsa wanda ya sa kwamitin mutum biyar daga shiyyar gudanar da bincike tare da gano tushen lamarin, kimanin makonni biyu da suka gabata,” in ji shi.
Kyari, ya ce an kafa kwamitin da zai binciki lamarin inda ya ce kwamitin ya gayyaci Sanatan amma bai iya kare kansa daga zargin ba don haka kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shi daga jam’iyyar.
Ya ce an dakatar da Abubakar ne bisa shawarwarin kwamitin ladabtarwa da ya same shi da laifukan cin zarafin jam’iyya.
Kyari ya ce kwamitin zartarwa ta APC a jihar ne ya amince da dakatar da ‘yan majalisar.