Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta cafke matasa bakwai (7) bisa zarginsu da kasance ‘yan daban da suke addabar jama’a da aka fi saninsu da ‘yan Sara-Suka.
A wata sanarwar da Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Sufuritendan Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Lahadi na cewa, bincike ya nuna cewa wadanda aka kaman ana zarginsu ne da kasance ‘yan kungiyar dabanci da ake kira da ‘Sara-Suka’ wadanda suka addabi al’ummar cikin kwaryar Bauchi.
A cewarsa wannan matakin ya biyo bayan umarnin da kwamishinan ‘yansandan jihar ya bai wa kwamandojin yanki-yanki, DPOs da jami’an dakile bata-gari da su tabbatar sun kutsa kai lunguna da sakona na maboyar ‘yan ta’adda domin tabbatar da an gudanar da bikin Ista cikin kwanciyar hankali a fadin jihar.
A fadinsa, a ranar 08/04/2023 jami’ansu da hadin guiwar wasu jami’an tsaron sun samu rahoton sirri inda suka yi dirar mikiya ga maboyar ‘yan daban da ke cikin wata ginin da ba a kammala ginawa a unguwar Magaji Quarters tare da taso keyar matasan.
Wadanda aka kama din su ne: Rayyanu Mohammed Dan shekara (25) Mustapha Harisu (19); Yusuf Ibrahim (Mai shekara 18); Mubarak Lawal (18); Abubakar Musa (18); Al-Amin Hussaini (20); da kuma Hamza Umar (17) dukkaninsu mazauna Magaji quarters Bauchi.
A kan haka, an kwato makamai iri-iri da wasu abubuwan sha daga hannunsu yayin farmakin da suka hada da gatari guda biyu; wukake uku; kwalabe goma mara komai na maganin tari da ke sanya maye; kunshi daya na tabar wiwi da dai sauransu.
Sanarwar ta kara da cewa, bincike na cigaba da gudana kuma za su kara zafafa bincikensu kan lamarin, bayan sun kammala kuma za su gurfanar da su a gaban kuliya mance sabo.
Wakil ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan jihar CP Aminu Alhassan ya shawarci iyayen da suke sanya ido kan harkokin ‘ya’yansu domin karesu daga fadawa munanan ayyuka.