‘Yan sanda a Jihar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka sace a karamar hukumar Toungo ta a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana haka a Yola a ranar Litinin cewa yana daya daga cikin nasarorin da rundunar ‘yan sandan ta samu na hada kai wajen kawo karshen garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.
- Za Mu Ceto Mutanen Da Aka Sace A Zamfara —’Yan Sanda
- Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu
“An kashe wani mai garkuwa da mutane a lokacin da shi da ‘yan kungiyarsa suka isa wurin karbar kudin fansa Naira miliyan biyu da aka nema daga ‘yan uwan wadanda suka sace.
“Wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hango jami’anmu a kusa da unguwar inda suka yi musu ruwan wuta.
“An kashe daya daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da raunukan harsashi,” in ji shi.
Nguroje ya kara da cewa an ceto mutanen biyu Suleiman Abdullahi (23) da Ruwa Buba (11) mazauna kauyen Mayo Sumsum da ke karamar hukumar Toungo.
Ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan Adamawa, Mista Afolabi Babatola, ya yaba wa jami’an ofishin ‘yan sanda na Toungo da mafarauta kan kokarin da suka yi.
Babatola ya umarci rundunar hadin guiwa da ta zakulo ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane da suka gudu don tabbatar da cewa ba su sake haduwa a ko ina a jihar ba.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci mazauna yankin da su rika sanar da ‘yan sanda inda masu aikata laifuka suke, musamman wadanda aka samu da raunukan harsashi,” in ji Nguroje.