ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Ceto Mutanen Da Aka Sace A Zamfara —’Yan Sanda

by Sadiq
3 years ago
Zamfara

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya tura karin tawagar jami’an’yan sanda don ceto mata da kananan yara da ‘yan bindiga suka sace kwanan nan.

A cewarsa, wasu ‘yan bindiga da suka gudu ta hanyar Kucheri-Wanzamai-Gidan Chida a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara sun yi garkuwa da mata da yara a yankin.

  • Allah Ta’ala Ya Alakanta Azumi Da Kansa (SWT)•Yadda Azumin Ya Dara Sauran Ibadu
  • Allah Ya Yi Wa Mai Dakin Aminu Dantata, Hajiya Rabi Rasuwa

Leadership Hausa ta samu cewa wasu gungun ‘yan bindiga da suka tsere daga Jihar Zamfara sun yi awon gaba da dimbin jama’a daga kauyuka uku na Wanzamai, Gidan Chida da Kucheri. Galibin wadanda aka yi garkuwa da su kananan yara ne da ke aiki a gonakinsu a kauyukansu. Wasu daga cikinsu sun fito ne daga al’ummar Yankara da ke karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina.

ADVERTISEMENT

Leadership Hausa ta kuma samu labarin cewa kwanaki kadan kafin wannan aika-aikar da aka yi garkuwa da jama’a, wata tawagar jami’an soji ta kashe wasu ‘yan bindiga guda hudu da ake zargin ‘yan bindiga ne a wani samame da suka kai a unguwar Gidan Damo da ke karamar hukumar Tsafe.

A cewar wata majiya ta kusa da rundunar sojin, dakarun Operation Hadarin Daji sun kaddamar da hare-haren ba-zata a dajin Rugu tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama inda suka tilasta musu barin matsuguninsu. An ba da rahoton cewa, ‘yan bindiga da dama sun samu raunuka daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ta bukaci mazauna jihar da su yi watsi da wannan munanan kalamai da ake yadawa a wasu sassan kafafen yada labarai.

Rundunar ‘yan sandan ta kara tabbatar wa jama’a musamman iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, cewa tana aiki tare da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga domin kubutar da wadanda lamarin ya shafa tare da hada su da iyalansu.

MASU ALAKA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe
Manyan Labarai

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Next Post
Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu

Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu

LABARAI MASU NASABA

Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

July 17, 2026
Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.