Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, gwamnatinsa zata mayar da layin samar da wutar lantaki na kasa na bai daya ta hanyar farfado da kanan layin samar da wutar.
Gwamnati za ta yi haka ne domin ta magance kalubalen da ake fuskanta na samar da wadacacciyar wutar a daukacin fadin kasa.
- Farashin Kalanzir Da Gas Ya Karu Da Kashi 88 A Cikin Shekara Daya – NBS
- Majalisar Dattawa Zata Tantance Sunayen Ministocin Buhari Ranar Laraba Mai Zuwa
Shugaban ya sanar da hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wata kafar yada labarai, ya ce, gwamnatinsa ta ware dala miliyan 550 domin samar da wutar sola ta tsarin (SHS) 20,000 tare da samar da wutar sola ta tsarin (SHS) guda 250.
A kwanakin dai an sha fuskantar lalacewar babban layin samar da wutar lantarkin ta kasa, inda hakan ya janyo tashin gwaron zabin kudin man Dizil a kasar nan.
Shugaba Buhari ya ce, akwai ayyuka kusan guda dari da ake ci gaba da yinsu ciki har da aikin (PPI) da ke karkashin kulawar Fadar Shugaban kasa wanda ake yinsa a tsakanin gwamnatin Nijeriya da gwamnatin kasar Jamus wanda kamfanin kasar Jamus ‘Siemens AG’, ke yi don a kara inganta layin samar da wutar.