Abokai, kwanan baya wasu manyan jami’an kasa da kasa sun kawo ziyara nan kasar Sin, ciki hadda shugaban kasar Faransa da shugabar hukumar gudanarwar EU, sai kuma firaministan Singapore da na Malaysia da na Spaniya da ministan harkokin wajen Japan da sauransu. Abin dake nuna cewa, Sin tana mu’ammala da kasashen duniya sosai.
A halin yanzu, ana fuskantar rashin tabbas da kalubaloli a duniya, shi ya sa hadin kai da samun moriya tare ya zama burin da kasa da kasa ke neman cimmawa, wadanda kuma suka fahimci cewa, kulla kawance mai kare muradun kashin kansu ko katse hulda ko yakin cacar baka, ba su dace da halin da duniya ke ciki yanzu ba. Kazalika, ganin yadda kasar Sin take kara bude kofarta ga ketare da ci gaban da take samun a bangarori daban-daban, ya sa shugabannin kasa da kasa na kara amincewa da makomar hadin kansu da kasar Sin da samun moriya tare.
Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da bunkasuwar tattalin arziki Navid Hanif ya taba shedawa manema labarai cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kawar da talauci, raya masana’antu da sabbin fasahohi, kana tana da gogewa masu tarin yawa, da za ta iya rabawa ga duniya. Ya ce, shawarar raya duniya da Sin ta gabatar ta nuna kyakkyawan fata da alkawarin da ta yi wajen inganta ci gaban duniya.
A halin yanzu, kasar Sin na kokarin farfadowa daga illar COVID-19 da kara mu’ammala da kasashen duniya, Sin mai sanin ya kamata, kuzari da bude kofa, da neman hadin kai da samun moriya tare, za ta zama babban tushe ga bunkasuwa da dorewar duniya. (Mai zana da rubuta: MINA)