A yau Laraba ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata sanarwa mai kunshe da ayoyi 11, wadda ke bayyana matsayin kasar Sin game da batun Afghanistan.
Sanarwar mai taken “Matsayar Sin game da batun Afghanistan” ta ce a halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi Afghanistan ta zamo dandalin hadin gwiwar sassa daban daban, maimakon wani wuri na ja-in-ja tsakanin sassan kasashen duniya. Kaza lika Sin na goyon bayan dukkanin matakai, da tsare-tsaren da suka wajaba, na warware batun Afghanistan ta hanyar siyasa.
A wani ci gaban kuma, a yau din kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, Afghanistan ta sha fama da wahalhalu masu tarin yawa, kuma a yanzu tana cikin wani muhimmin lokaci na fita daga rudani zuwa samar da managarcin jagoranci.
Wang, wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da batun, ya ce domin fahimtar cikakkun manufofin kasar Sin, da shawarwarin da ta gabatar, da burin ta na cimma matsaya, da hada hannu da sauran sassan kasa da kasa, da kasashen yankin ta, wajen wanzar da daidaito da taimakawa Afghanistan, Sin din ta tsara, tare da fitar da sanarwa game da hakan. (Saminu Alhassan)