ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Kasashe Da Yawa Ke Warware Tasirin Dalar Amurka?

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A cikin kwanakin baya, kasashe da dama na daukar matakai a kokarin warware tasirin dalar Amurka, ciki har da kasashen Latin Amurka, da na gabas ta tsakiya, sai kuma kasashen ASEAN, da Rasha da Iran, har ma da wasu kasashen Turai, bi da bi sassan suna ta bullo da shirye-shiryensu, ko kuma daukar matakai, don neman gudanar da ciniki da kudaden da ba dalar Amurka ba. A Afirka ma, gwamnatin Kenya ta sanar da yin watsi da dalar Amurkar wajen shigar da makamashi, inda har ta cimma yarjejeniya da kasar Saudiyya, kan sayen makamashi da kudinta na shilling. Ita kuwa ministar harkokin wajen kasar Afirka ta kudu Naledi Pandor cewa ta yi, kasashen kungiyar BRICS na nazarin kafa wani tsarin ciniki mai adalci bisa bankin NDB wanda aka kafa a shekarar 2014, ta yadda za a kai ga warware tasirin dalar Amurka. 

Amma me ya sa kasashen ke wannan kokari? Lallai tun bayan da dalar Amurka ta kafa babakere a duniya bisa tsarin Bretton Woods da aka kafa a shekarar 1944, kasashen duniya sun sha wahalhalun da dalar ta haifar musu. Kasancewar dala muhimmin kudin da aka fi yin amfani da shi wajen gudanar da ciniki tsakanin kasa da kasa, Amurka ta sha yin amfani da dala wajen kakaba takunkumi a kan wasu kasashen da suka ki biyayya gare ta, baya ga yadda ta rika cusa matsalolin tattalin arzikinta ga sauran kasashen duniya, tare da kwace arzikinsu ta hanyar daidaita kudin ruwa kan dala.

  • Wariyar Launin Fata Da Amfani Da Makamai Barkatai Ne Ke Rura Wutar Harbe-Harben Kan Mai Tsautsayi A Amurka

Idan ba a manta ba, bayan aukuwar rikici tsakanin Ukraine da Rasha, Amurkar ta hada kan kasashe da dama wajen kakaba wa Rashan takunkumi, matakin da ya haifar da mummunan tasiri ga cinikin fitar da hajojin kasar, kuma hakan ya nuna yadda take amfani da dalarta a matsayin makami na nuna fin karfi.

ADVERTISEMENT

Sai kuma daga watan Maris na bara, asusun ajiyar kasar Amurka ya sha daga kudin ruwa har sau tara, a yunkurin daidaita matsalar hauhawar farashin kaya da take fuskanta a gida, matakin da ya haifar da hauhawar farashin kaya, da tabarbarewar tattalin arziki a kasashen duniya da dama. Kamar dai yadda yadda tsohon sakataren kudin kasar ta Amurka John Connally ya fada, “dala kudinmu ne, amma kuma matsala ce gare ku.”

A gabanin yadda kasashen duniya ke daukar matakai na warware tasirin dala, dan majalisar dattawa daga jihar Florida Marco Rubio, ya bayyana bakin cikin sa yana cewa, “Nan da shekaru biyar masu zuwa, babu zancen takunkumi, kasancewar karin kasashe na ciniki da kudin da ba dala ba, a gaba ba wani mataki da za mu iya dauka don sanya musu takunkumi.”

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

Abin haka yake, zamanin da Amurka ke amfani da dalarta wajen kafa babakere a duniya na dab da karewa, kuma ya kamata ‘yan siyasa irinsu Marco Rubio, su yi tunani sosai a kan me ya sa sassan kasa da kasa ke neman warware tasirin dala. In dai har Amurka ta ci gaba da nuna fin karfi da babakere, kuma ta gudanar da harkoki ba bisa ka’idojin duniya ba, tare da haifar da mumunnan tasirin ga tattalin arzikin duniya, to, tabbas za ta ga bayan matsayin dalarta. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 
Daga Birnin Sin

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

November 13, 2025
Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
Daga Birnin Sin

Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

November 13, 2025
An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
Daga Birnin Sin

An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

November 13, 2025
Next Post
Amurka Za Ta Iya Daidaita Batun Bazuwar Bayanan Sirri Kuwa?

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025
An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025
NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane

NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane

November 13, 2025
Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

November 13, 2025
Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

November 13, 2025
Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau

Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau

November 13, 2025
‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026

‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.