Yanzu haka dai majalisar wakilai na kokarin kafa dokar da za ta hana likitoci kasar waje har sai sun yi shekara biyar bayan sun kammala karatunsu.
Wannan matakin da majalisar ke kokarin dauka ya biyo baya ganin yadda likitocin ke turuwar zuwa kasashen waje domin yin aiki a can.
- Ministocin Wajen Kasashen Sin Da Rasha Da Pakistan Da Iran Sun Tattauna Game Da Batun Afghanistan
- Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Bunkasa Da Kaso 4.8% A Rubu’in Farko Na Bana Duk Da Raguwar Bukatun Waje
Ficewar likitocin wani babban kalubale ne ga al’ummar Nijeriya wanda hakan ya sa kasar fuskantar karancin ma’aikatan lafiya.
Wanna hali da aka fada na ficewar likitocin babban koma-baya ne a shanin kiwon lafiyar al’ummar kasar nan.
Kamar yadda Hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayyana Njeriya na fuskantar barazanar babba ta ficewar likitocinta.
Majiyarmu ta tabbatar mana da likitocin ke fita zuwa kasashen tarayyar Turai.
Jami’an lafiya sun tabbatar da cewa, a kalla likitoci 5,600 daga kasar nan suka tafi tarayya Turai a cikin shekara takwas da suka wuce.
A shekara ta 2022, kungiyar likitoci ta Nijeriya ta ce za a samu kima-baya a fannin lafiya matukar gwamnati ba ta dauki matakan da suka kamata ba wajen kawo karshen ficewar likitocin ba. Saboda haka kungiyar ta bukaci gwamnati ta gaggauta kawo karshen ficewar likitocin.
Haka kuma a farkon wannan shekarar shugaban kungiyar likitocin na kasa kuma shugaban kungiyar likitocin hakora Dakta Bictor Makanjuola ya bayyana cewam fiye da likitoci 500 suka bar kasar nan cikin shekara biyu da suka wuce .
Saboda haka kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Kaduna ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin kawo karshena kwararewar liktocin daga jihar Kaduna. Kungiyar ta nuna cewa,kusan likitoci 10,000 suka tafi wasu kasashe.
Su ma kungiyar gwamnonin kasar nan sun nuna damuwarsu kan yadda likitocin ke fita.
Shugaban kungiyar Aminu Waziri Tambuwal,ya nuna damuwarsa kan ficewar likitocin, da kuma yadda za samo bakin zaren, lokacin da ya ziyarci ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire, a Abuja.
Zaben Shugabanin Majalisa: An Nemi APC Ta Daidaita Tsakanin Kudu-maso-kudu Da Arewa-maso-yamma
Akwai yiwuwar jam’iyyar APC ta raba mukamin shugaban majalisa da mataimakinsa tsakanin Kudu-maso-kudu da shiyyar Arewa-maso-yamma.
Koda yake har yanzu jam’iyyar ba ta fitar da wata matsaya ba kan shugabancin majalisat ta 10 ba, sai wasu kafofi daga fadar shugaban kasa, sun nuna cewa, shiyyar Kudu-maso-kudu na iya samun shugaban majalisar.
Jam’iyyar APC ta samu nasara kujeru 57, yayin da ita kuma PDP, ke da guda 27.
 Sauran su ne LP da ta samu 6; NNPP ta samu 2; da SDP, 2, sai YPP da APGA wadda kowanneneu ta samu 1.
Zuwa yanzu wadanda ke sa ran za su iya samun samun shugabanci majalisar ta 10 sun hada da shugaban majalisar na yanzu Ahmad Lawan na jam’iyyar APC, daga Yobe ta Kudu sai Sanata Sani Musa na APC daga Neja-ta-gabas sai Sanata Chief Whip sai Sanata Orji Uzor Kalu na APC daga Abiya ta arewa sai Sanata Jibrin Barau na APC daga Kano ta Arewa sai Sanata Godswill Akpabio na APC, Akwa Ibom ta Arewa-mas-yamma.
Sai kuma Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Abdul Ningi na APC daga Bauchi ta tsakiya da kuma Sanata Abdul- Aziz Yari na APC daga Zamfara).
Haka kuma gwamna Dabid Umahi na APC da Ebonyi South da Adams Oshiomhole na APC daga Edo ta Arewa dukkaninsu sun nuna sha’awar zama shugaban majalisar.
Haka kuma Sanata Ali Ndume daga Borno da Sanata Osita Izunaso daga jihar Imo su ma sun nuna sha’awarsu.
Sai dai har zuwa wannan lokaci jam’iyyar na ci gaba da tuntuba kan shugabancin majalisar yadda za ta tabbatar da wanda zai bayar da cikakkiyar gudummowa wajen bunkasa kasa da hada da zababben shugaban kasa Bola Tinubu don samun ci gaba.