Babban jami’in hukumar INEC, Dr. Abacha Melemi na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gashu’a (FUGA), shi ne ya jagoranci zaben 2023 a lokacin da yake sanar da sakamakon a yau a garin Potiskum.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta ayyana Sanata Ibrahim Mohammed Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben, wanda ya gudana yau Asabar, a Yobe ta kudu.
Sen. Bomai na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 69,596 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Hon. Halilu Mazagane, mai kuri’u 68,885. Sauran sun hada da Hon. Yerima Adamu na ADC 652, Hon. Jauro Ishaku LP 471, Isa Musa NNPP 3,277 da Maisambo Barde na jam’iyyar YPP mai kuri’u 448.
A sa’ilin da yake bayyana sakamakon zaben, a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE. T) dake Potiskum, Dr. Abacha Melemi ya ce, “Nine Abacha Melemi, jami’in hukumar INEC mai kula da zaben 2023 na mazabar Sanatan Yobe ta kudu, zaben da ya gudana ranar 15 ga watan April, 2023, wanda ya nuna Bomai Ibrahim Mohammed na jam’iyyar APC shi ne ya cika dukan ka’idar da doka ta tanada, wanda saboda haka na ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.”
A lokacin da yake jawabi, jim kadan da bayyana sakamakon, Sen. Ibrahim Mohammed Bomai ya nuna godiyarsa ga al’ummar Yobe ta kudu bisa gagarumin goyon bayan da suka bashi wajen samun wannan nasara da yayi.
Har wala yau, Bomai ya bayyana godiyarsa da jinjinawa Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC dangane da goyon bayansu zuwa ga samun nasara.