A jiya ne, mai dakin shugaban kasar Xi Jinping, Peng Liyuan, ta gana da Rosângela Lula da Silva, uwargidan shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Uwargida Peng ya ce, duk da nisan da ke tsakanin kasashen biyu wato Sin da Brazil, al’ummomin kasashen biyu suna da zuciya daya, kuma suna jin dadin hadin gwiwa da mu’amalar al’adu daban-daban.
Peng ya gabatarwa Rosângela tarihi da al’adun kasar Sin, da kuma kyawawan fasahohinsu daban-daban. Ta kuma yi fatan cewa, Lula da Rosângela za su ji dadi tare da samun sakamako mai kyau a ziyarar da suka kawo, tare da fatan karfafa abota mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.
A nata bangare kuwa, uwargida Rosângela ta godewa shugaba Xi da mai dakinsa Peng, bisa karramawar da suka yi mata, tana mai cewa, ko da yake wannan ita ce ziyararta ta farko a kasar Sin, amma ta riga ta ji cewa, kasar Sin kasa ce mai dogon tarihi da kyawawan al’adu gami da kuzari na zamani. Ta bayyana aniyarta ta zurfafa fahimtar kasar Sin da inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)