A halin yanzu da aka kammala babban taron manyan jam’iyyu Nijeriya, tare da fitar da wadanda za su yi masu takarar shugabancin kasa a zaben 2023.
A daidai lokacin da aka fara fafutukar yakin neman wanda zai tsaya wa kowacce jam’iyya takarar mataimakin shugaban kasa, ‘yan Nijeriya musamman talakan da yake a karkara ya ga yadda ‘yan siyasa suka rika kece raini da nuna isa wajen wasa da kudade, musamman ma ta yadda kudi ne ya zama manuniyar wanda zai zama dan takarar a matakai daban-daban a jam’iyyunmu, wato wanda ya fi bayar da kudi shi ne ke da tabbas na tsayawa takarar da ya shiga ba wai cancanta ba.
Kasancewar jami’an hukumar EFCC a wuraren tarukan bai yi wani tasiri ba, zuwan su ya zama kamar wata farfaganda ce kawai amma su wadannan ‘yan siyasar basu dauke su da wani muhimmanci ba, haka dai jami’an EFCC suka kasa yin komai dangane da yadda ake kashe kudi a kan wakilai masu zabe (Deliget).
A bayyane lamarin yake cewa, wadannan ‘yan siyasar da kudaden gwamnati suke tinkaho wajen sayen masu zaben, inhar da a wasu kasashe ne irin wannan halayyar ke faruwa lallai ya isa ya zama dan siyasa ya fadi warwas a zaben da ya yi takarar.
A haka al’umma suka yi ta kallo suna tunani a zuciyarsu ko yaushe wannan cin fuskar zai kare su cigaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da yadda shugabanni ke cin masara a gabansu suna jefa musu totuwar ba.
A ra’ayin wannan jariar, yana da muhimmanci a lura da cewa, akwai abubuwa da dama da ke faruwa a wannan tsari na dimokradiyya wadanda ke kai ga jefa kokwanto a zukatan al’umma na cikakken sahihancin wannan tsari na tafiyar da mulki da muke amfani dashi a kasar nan a halin yanzu.
Alama ta farko da ke nuna lallai akwai matsala shi ne yadda ake wulakanta kudin Nijeriya, wato Naira, a halin yanzu ‘yansiyasan Nijeriya basa jin sun cika sai sun fara kashe kudaden kasashen waje wato Dala ko Fam. Dala ake rabawa a kokarin jawo hankulan wakilai masu jefa kuri’a, yanzu Dala ya zama alami na karfi a fagen kama mudafun iko a fadin tarayyar Nijeriya.
A wannan lokaci na tarukan manyan jam’iyyu an ga yadda Deliget suka rika zama Miloniya a farat daya, a wani bangare kuma ‘yan Nijeriya sun rika raha da al’amarin abin kuma da yakamata ya zama wani tashin hankulla da abin kunya ga al’ummar Nijeiya gaba daya.
Ya kuma kamata a lura cewa, a daidai wannan lokacin da ‘yan siyasa ke cin kasuwarsu babu batun tsananin rashin aiki da matasanmu ke fusanta a zukatansu haka kuma al’amarin tabarbarewar tattalin arzikin kasa samsam bashi a tsarin su, ballatana su tattauna yadda za a yi maganinsa.
Sun yi watsi da tattauana abin da ya shafi matsalar tabarbarewar tsaro da ake fuskanta a sassan Nijeriya, wannan ya sa ake tunanin ko shugabnin kasar nan na murna da halin da ake ciki ne na rashin tsaron ne a Nijeriya.
Abin tayar da hankali a nan shi ne yadda harkokin rayuwa ke tsada a daida lokacin da kuma ‘yan siyasa ke kara bayyana irin rayuwa na allubazanranci da suke yi da kudaden alummma, sun danne bukatun al’umma a kan nasu bukatun. Ayyukan ta’addanci, kamar garkuwa da mutane da kashe-kashe sai karuwa suke yi a kullum, duk wannan ba abin damuwar ‘yan siyasar mu ba ne.
Abin bantsoron kuma shi ne ‘yan siyasar namu ba a bin da ya dame su da halin da iyaye suke ciki na zaman gidan da yaransu ke yi sakamakon rikicin da ke tsakanin Gwamnati da kungiyar Malamai ta ASUU. Dan abin da Malamam jami’ar suke nema ya yi yawa amma sai gashi ana rokon Deliget su karbi makudan kudi wanda ya isa gina jami’o’i da dama a fadin kasar nan.
A namu tunanin, a wurin ‘yan siyasa lamarin da ya shafi gyara hanyoyi da makarantu da asibitoci duk suna iya dakatawa har sai an zabi jerin wasu masu handamar da za su jagoranci kasar nan.
To yanzu da yake an kai ga zaban wadanda za su shiga gwagwarmayar kuma an kammala rabe-raben kudaden, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su natsu su kuma jagoranci wadanda tantance mutane tare da dubi ga irin ayyukan da suka yi a rayuwar su, ayyukan bunkasa rayuwar al’umma ta haka za su kai ga zaben wadanda suka fi cancanta ba wai maganar wanda ya fi bayar da kudi ba.
Wannan jaridar na kira ga ‘yan Nijeriya su ba mara da kunya, su nuna cewa sun san siyasa yadda yakamata, su nuna cewa, sune masu zaba tare da kafa wanda suka ga ya dace a kan karagar mulki.
Idan ana son cimma wannan kudurin to dole a cire duk wani abin da ya shafi banbancin addini da kabilaci wajen zaban dan takara, a fuskanci mutum da irin ayyukan da ya yi a baya da kuma wanda ya shirya gabatarwa a nan gaba.
Wannan jaridar na da ra’ayin cewa, lokaci ya yi da al’umma za su yi amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya basu na zaban mutane kirki da za su jagoranci kasar nan.