ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ra’ayoyinku A Kan Ko Atiku Abubakar Da PDP Ta Tsayar Zai Iya Kai Bantensa A Zaben 2023?

by Aisha Seyoji
4 years ago
Atiku Abubakar

Barkanmu da sake saduwa a filinmu na Ra’ayi Riga,Wannan mako za musgabatar muku da ra’ayoyinku ne a kan tsayar da Atiku Abubakar da aka yi a matsayin dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar PDP a karshen makon jiya, shin a ganinku zai iya kai bantensa kuwa.

Man Nass
Wannan shi ne abin da muka fi kyautata masa zato musamman a wannan lokaci da mutane suke cikin matsanancin rayuwa wanda gani ake yi kamar jam’iyya mai mulki bata yi wa al’umma abinda zai rage musu radadi ba.

  • INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka’idojin Zaben 2023

Bashir Ibrahim Matazu
Idan an yi aiki tukuru zai iya kai labari idan kuma ‘yan PDP suka maida hankali ak an zagin wasu da suke hamayya za su iya komawa gidan jiya. Allah Ya ba mai rabo sa a.

ADVERTISEMENT

Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Allah wadaran na ka ya lalace… A wannan filin mai albarka mun tattauna magana a kan zaben fidda gwani, inda mu ka ce Delegets su yi gaskiya amma sai gashi labara ya zo cewa, Atiku ya kashe su da iyayen kudade sun zabe shi.
Don haka Atiku zai iya kaiwa ga ci, tun da lamarin na kudi ne, Allah ya ba mu shuwagabanni na gari.

Omar Naseer Imam
Muna fatan Atiku ya zama alkhairi a gare mu duk da bamu da zabi fatanmu Allah ya bamu wanda zai zama mafita ga al’umman Nijeriya gaba daya, arewaci da kuma kudancinta Alfarman Annabi Muhammad (SAW)

LABARAI MASU NASABA

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

Sani Bello Kano
Wallahu galibun ala amrihi, to babban abin dubawa anan shi ne yadda yake sakarwa deligets kudi kamar hauka, sannan kuma indai a haka za a tafi to lallae zai iya samun mulki tunda sai abinda suka ce sannan kuri’ar talaka bata da amfani sai abinda INEC suka ce, sannan kuma suma ba zai barsu haka ba, sai dai addu’ar Allah ya zaba mana mafi alkhairi.

Cmrd Sadeek Rufa’i Ɗanguguwa
Allah wadaran Zaben fidda gwani irin wannan. Duk da irin kiraye kiraye da gidan Jaridu da malamai suka yi ta yi wurin tsarkaka niyya ga dukkan masu alhakin fidda dan takara, amman sai da suka kauce ta hanyar amsar kudade. Allah ya kyauta wannan lamari.

Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya mutane sun sha wahala a wannan mulkin na APC duba da yanayin kuncin rayuwa da ake ciki to idan akai duba da hakan zai iya kaiwa ga nasara. Amma mu yawancin ‘yan Nijeria mun tura lamarin ga Allah ne domin zabin Allah shi ne zabi. Mudai Allah ya zaba mana shugabanni nagari, idan shi ne alkairi Allah ya bamu ikon zabarsa.

Ibrahim Hassan Baban Adila
Anawa tunanin inaga Atiku Abubakar zai iya kai labari duba da duk ‘yantakarar da suka fito basu da karfin da za su kara dashi, sannan kuma yadda analysis yanuna yawancin yan arewa za su yi Atiku kuma yankin arewa sun fi kudu yawa sosai, sannan mutane sun gaji da jam’iyyar APC sakamakon gazawar da ta yi wajen mulki, abubuwa sun tabarbare ba kamar yadda suka zo suka sami kasar ba. Daga karshe mu talakawa muna rokon Allah ya zaba mana shugaba nagari kuma mafi alkhairi a gare mu Amen, daga Ibrahim Hassan Minister Baban Adila da ansar Jihar Gombe.

Muhd Basheer Sa’ad
Duba da yadda al’amura suka tabarbare wa Shugaba Buhari tabbas APC za ta sha kayi ne.
Shi kuwa Atiku shima ba wani labari da zai kai duk da cewar yana da magoya baya.
Allah dai ya zaba mana shugaba mafi alhairi ga rayuwar mu, amin

Sani Ladan
To lallai wannan batu na takarar Atiku babbar nasara ce ga yankin mu na arewa kuma gaskiya wannan karon Atikun zai iya kai bantensa a kakar zabe mai zuwa duba da yadda ita jam’iyya mai mulki ta Gaza sauke nauyin da yake kanta,muna fatan Allah ya zaba mana mafi allhairi

Saimas Spices
Gamu nan dai kuma a game na siyasar Nijeriya, bamu da ikon jayyaya da deligete wanda idan ba an canza tsarin zaben deligates din bama siyasa ba za ta gyaru ba, mu dai talakan Nijeriya zamu ci gaba da addu’ar Allah ya zaba mana mafi alkhairi

Maman Aisha
To ai wannan abin sai Allah kawai, sai dai fatan mu Allah ya bamu nagari wanda zai yi abinda ya dace damu ‘yan Nijeriya, Allah ya ba mu sa a

Moubarak Abdoullahee
Aslm mudae ayanzu bazamu iya fadan cewa ze iya kai bantennasaba ko Aa, harsemunga yadda ta kaya azaben fidda gwani na jam iyar APC domin ance darashin uwa ake uwar daki

Nura Usman Idris
Da wahala gaskiya duba da yadda Talakawa suka yi masa bakin fenti.

It’z Sam Dambatta
To ita dai siyasa mace ce da ciki amma gaskiya abin da kamar wuya, musamman idan a kace jagoran kwankwasiya ya tsaya a jam’iyar NNPP. Mu dai fatan mu Allah ya zaba mana mafi alkhairi

Khadija Muhammad
Zabin Allah shi ne zabi, Allah ya zaba mana mafi alhairi

Atiku Abubakar
Aisha Seyoji
+ postsBio
  • Aisha Seyoji
    https://hausa.leadership.ng/author/aisha-seyoji/
    Mata Mu Kara Hakuri A Zamantakewar Aure -Aisha Seyoji
  • Aisha Seyoji
    https://hausa.leadership.ng/author/aisha-seyoji/
    Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?
  • Aisha Seyoji
    https://hausa.leadership.ng/author/aisha-seyoji/
    Ra’ayoyinku A Kan Ba Da Bashi Ga Daliban Manyan Makarantu
  • Aisha Seyoji
    https://hausa.leadership.ng/author/aisha-seyoji/
    Abin Haushi, Mata Sun Mayar Da Maza Tamkar Bola

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe
Siyasa

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM
Siyasa

‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

June 3, 2026
Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al’ummar Nasarawa – Wadada
Siyasa

Gwamnatina Za Ta Mayar Da Hankali Kan Buƙatun Al’ummar Nasarawa – Wadada

June 1, 2026
Next Post
2023: Ta Tabbata Kauran Bauchi Ne Dan Takarar PDP A Gwamnan Bauchi

2023: Ta Tabbata Kauran Bauchi Ne Dan Takarar PDP A Gwamnan Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Ana Gudanar Da Taron Masana Ilmin Harkokin Kasar Sin Karo Na Uku

Ana Gudanar Da Taron Masana Ilmin Harkokin Kasar Sin Karo Na Uku

June 4, 2026
Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.