Babban Bankin Stanbic IBTC, na daga cikin babbar cibiyar hada-hadar kudi a Nijeriya, ya yi bikin karrama wadanda suka lashe kyautar ‘Reward4Sabing Promo Season’ zango na 2, a wani gagarumin wasan karshe da aka gudanar kwanan nan a babban ofishinsa da ke Legas.
Garabasar, wacce ke da nufin habaka ceto al’adu tsakanin ‘yan Nijeriya, an bude shi ne musamman ga sababbin abokan ciniki na da da na yanzu.
Domin shiga tsarin, an shawarci kwastomomin da su saka kudi har Naira 10,000 a asusun ajiyarsu, sannan su bar shi na tsawon kwanaki 30 don samun ladan tsabar kudi daga Naira 100,000 zuwa Naira 2,000,000 a cikin tsarin hada-hadar kudi ta intanet.
Karo na biyu na garabasar ya bai wa kwastomomi 840 kyautar Naira 100,000 kowanne, 28 kowannen su ya samu Naira 1,000,000, sai bakwai da suka samu Naira 2,000,000 kowannensu. Dukkan wadanda suka yi nasara an zabo su ne ta kafar intanet, tare da Hukumar Kula da Lottery ta Kasa da Hukumar Tallata (AW1) ta Nijeriya don tabbatar da tsari na gaskiya.
Babban Daraktan Bankin Stanbic IBTC, Olu Delano, ya bayyana jin dadinsa da kwazon duk wanda ya halarci gasar ta 2.
Ya yaba wa wadanda suka yi nasara a gasar, ya kuma bukaci kowa da kowa da ya samu kwarin gwiwa daga irin wannan gagarumin aikin da suka yi na tanadi na tsawan lokaci, tare da misalta dabarun hada-hadar kudi da kuma jajircewa wajen cimma manufofinsu na kudi.
“Muna farin ciki da irin sadaukarwar da dukkan mahalarta taron a kakar wasa ta 2 suka yi.
Yawan kwararrun masu tanadi a kowane wata ya nuna cewa mutane na iya sadaukar da kansu don yin tanadi na dogon lokaci.
Kamar yadda kuka himmatu ga manufofin ku na kuzi, mun himmatu don tallafa muku wajen cimma su da kuma ba ku damar yin rayuwa mai inganci,” in ji Olu.
Shugaban bankin Stanbic IBTC, Wole Adeniyi, ya bayyana mahimmancin tallan na ‘Reward4Sabings’ wajen karfafa kwastomomi don adanawa da kuma ba su lada.
Ya jaddada cewa tallan ya yi tasiri ga rayuwar mutane da yawa yayin da tanadin kudade na ranakun damina ke da wahala saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Bankin Stanbic IBTC ya kuma sanar da cewa shirin garabasar ‘Reward4Sabing Season Promo’ zai ci gaba har zuwa kakar wasa ta uku, kuma ya bukaci kowa da kowa ya kula da cikakkun bayanai wadanda za a buga a tashoshin yada labarai na kan layi.