Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da shagulgulan Sallah, duba da yadda kowa ke nuna farin ciki a wannan lokaci na bikin sallah, ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin matasa game da irin tanadin da suka yi wa Bikin Sallah, hadi da jin irin shigar Ankon da za a yi a wannan Bikin sallah, musamman yadda kowacce shekara ake fitowa cikin shigar anko ga wadanda Allah ya horewa da kuma wadanda suke da sha’awar yi, ko a wannan shekarar akwai Ankon da ka fitar?, Wanne irin abinci da abin sha matasa ke bukatar ci a ranar Sallah?, Ko wacce irin shawarwari za a bawa sauran matasa gane da bikin Sallah?. Gadai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Siyama Abdul daga Jihar Kano:
Na yi wa sallah tanadin kwalliya ta musamman idan muna da yawan rai in sha Allah, bayan sallar idi, ina so na ci abubuwa da yawa kamar wainar shinkafa da Sinasir da miyar Agushi, zan ci fried Rice da paper chicken, da Lemon Kunun Aya da Zobo. Shigata ta ranar farko za ta kasance farar Shadda wadda aka yi mata rantsattsen jan aiki me taken Abbah Gida-Gida. Bayan nan sai ziyara gidan yayyenmu da kannen iyayyenmu, na kusa dana nesa, wanda kakanmu ne da kansa ya ke d’aukar mu kaf jikokinshi ya kai mu da kansa ba tare da driber ba. Gaskiya ban sani ba ko akwai anko a wannan shekarar mu dai za mu saka kayan da aka yi mana. Shawarata ga ‘yan bikin sallah matasa, ayi bikin Sallah cikin lumana, ba tare da neman tashin hankali ko hargitsi ba.
Sunana Khaleep Saleh Tabla daga Jihar Bauchi:
Ina so na je Yankari ni da budurwata domin nuna farin cikinmu, duk shekara muna anko duk ‘yan gidanmu, ankon gari kuma gaskiya ban sani ba. Ni dai ina farawa ne da Kunun Tsamiya da Masa. Ina kira da ‘yan uwana matasa da a rage gudu a kan abin hawa kamar; mashin da mota da dai sauransu, saboda kiyaye lafiyar mu.
Sunana Aliyu K/Ruwa daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment):
Kamar yadda muka saba bayan Sallar Idi mukan ziyarci ‘yan uwa 1 ga sallah zuwa 2, 3 mukan je gidajen wasanni domin nuna farin ciki hade da godiya ga Allah tare da fatan Allah ya maimaita mana.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi daga Jihar Kano (Dr.Hibbat):
A gaskiya wannan shekarar koma na ce wana sallah ina da burin zuwa Sallah, saboda na dauki lokaci mai tsayi rabo na da zuwa. Ankon sallah ya zama kamar duk shekara ne, wannan sallar ma akwai anko. Abin da nake son fara ci Dabino da kuma Tuwo, Shawarata ga matasa dan Allah samari da ‘yan mata a kula da kyau yayin hidimar Sallah, Allah ya raya mana yaranmu da kannenmu da ma duk wani mai rai da lafiya, Allah ya tsare mu baki daya ayi wasa lafiya, ya sa ayi taro lafiya, kowa ya koma gida lafiya, ina yi muku fatan alkhairi.
Sunana Ridwan Binna daga Jihar Kano Kamfanin Gwammaja Entertainmemt:
Wajen da zan je da Sallah zuwa gidan zoo kallon namun daji, zuwa gidan Makama, sannan kallon Sarki. Ankon da za a yi Maza Jallabiyya Mata Hijab mai fuska da hannu. Abincin da nake son ci Tuwan shinkafa da Miyar Kabewa ko Wainar Shinkafa, da drink. Shawarar da ya kamata kowanne matashi ya zama duk inda zai je ya kare mutunchinsa dana addininsa.
Sunana Sulaiman AK daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment);
Da sallah ina da burin ziyarar dangina, anko zai kasance Shadda, Abincin Sallah na fi san Tuwo abin sha lemo mai sanyi, shawarata ga matasa shi ne su ji tsoran Allah.
Sunana Hadiza Hussaini daga Maiduguri (Gwammaja Entertainment):
Zan je ziyara da gidajen hoto, ankon hijjabi ne, abincin da nake son ci Shinkafa da naman kaji, da 5 alibe, shawarata Matasa aji tsoron Allah, su nutsu kuma su yi hankali.
Sunana Ayuba Sulaiman daga Jihar Kano Nassarawa LGA Badawa Unguwar Gaya (Gwammaja Entertainment):
Tanadi na farko shi ne; zuwa masallacin idi domin shi ne abu na farko, sannan kuma ziyara zuwa wajen ‘yan uwa da abokan arziki. Anko kuma gaskiya ban ce wannan karon za a yi kamar yadda aka saba ba, saboda yanayi na yau da kullum. Shawarata zuwa ga matasa shi ne ayi Sallah lafiya a gama lafiya ba tare da hayaniya ba.
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse daga Jihar Kano:
Tanadin bai wuce sabbin kaya da ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki ba. Ai wannan Sallar babu wani anko daga Matan har Mazan, saboda yanayin da aka shiga tun kafin azumi. Abincu Tuwon Shinkafa da Naman Kaji. Matasa mu kula muyi abin da ya dace da al’ada da addininmu kada mu je mu aikata abin da Allah ya haramta mana, da sunan biki ko murnar Sallah.
Sunana Salma Ismail daga Jihar Kano (Gwammaja Enteetainment):
A kowacce Sallah ranar Edi ina fara cin Dabiyo da ruwa kafin in je masallaci. Inayi shiga irin wacce addini ya tanadar mana doguwar riga da Hijabi sababi. Shawarar da zan bawa matasa shi ne abi komai a hankali ayi bikin Sallah cikin ladabi da da’a. Na kan je gidajen ‘yan uwana da abokan arziki in ziyar ce su.
Sunana Abdulfata Idris Galadima daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment):
Ni da abokanai na mun shirya yin bazata wa ‘yan matanmu a Jabi dam, ni da abokanai na mun shirya yin dinkin shadda Malun-Malun, ‘Yan matanmu kuma za su sa Abaya. Zan so in sha abu ruwa-ruwa, kamar Hollandia da Kaza. Shawarata shi ne kowa ya tabbata ya ji dadi kuma yana cikin farin ciki.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Tanadin da aka yi wa ranar Sallah ta gobe yana da yawa, kamar ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki da sauransu. Ankon sutura kuwa na Maza ko mata wannan shekarar ma akwai abin da ba a rasa ba, don sai ranar sallah za a gani. Kalolin ankon samari da ‘yan mata yanada yawa kowanne jiha akwai abin da suka tsara za su yi. Wannan sallar ma ‘yan mata za su fita idi. Ni dai na fi son cin Tuwon shinkafa da miyar Agushi da Naman Kaji. Sannan abin sha kuma lemon Juice me sanyi ko Natural fruits ba lemon roba Kona gwangwani ba me gas. Shawara itaBce na farko suyi kokarin dawo wa gida da wuri bayan kammala sallar idi, sannan kaucewa duk shiga wani wuri da rigima ko fadan daba zai iya faruwa, sannan kula da wayoyinsu, musamman yayin daukar hotuna, bayan haka a yi shiga ta mutunci, wacce ta dace da addini da kuma al’adar Malam Bahaushe.
Sunana Habashiyya Abubakar Sa’id daga Jihar Kano Kofar Na’isa (Gwammaja Entertainment):
Tom! Gaskiya bikin Sallah yanada dadi ranaku ne na farin ciki da nishadi, da jin dadi da annashuwa, musamman ranar idi. Ina san ranar idi sosai saboda rana ce ta sada zumunci ga ‘yan uwan mu musulmai, masallahcin idin Kofar Na’isa yana daukar mutanan unguwanni da yawa abun yana burge ni, sannan shi idi ba a daukewa maza ko mata ko dattijai ko kananan yara ba, an fi so kowa ya halacci wajan saboda shi ne cikon ibadarmu na wata guda da Allah ya bamu iko muka yi.
Sunana Yahaya Yusuf daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment):
Abu na farko zan je Ziyara, zan saka fararan kaya sababbi, zan ci dabino, shawara a maida hankali akan ibada.
Sunana Isa Auwal Koki daga Jihar Kano (Gwammaja Entertainment):
Ni dai akan kaina ina so na fara shan shayi da tuwan shin kafa miyar Agushi. Shawarar da zan iya bawa matasa ai wasan sallah daidai misali ka da aje ai abun da bai dace ba.
Sunana Jamila Gamdare daga Gwammaja Entertainment:
Abin da yake burge ni a wasan sallah sanya Hijab zuwa sallar EDI da kuma kai yara gurin wasanni.
Sunana Abdulazeez Bin Musa daga Abuja (Gwammaja Entertainment):
Na yi tanadin shiga cikin sabbin kaya, tare da zuwa wuraren ziyara. Ina bawa matasa shawara a rage ganganci da abin hawa na ranar Sallah, abinci kuma ina so in fara cin naman kaza ta Hausa.
Sunana Yareema Shaheed (Dan Amar) daga Jihar Kano:
A wannan Sallah na yi tana din hawan bikin Sallah a masarautar Zazzau tare da yin tafiya zuwa ziyara gurin ‘yan uwa da abokan arziki. E! To wannan Sallar ya bambanta da sauran Sallah, domin matasa da dama ba su yi dinkin sallah ba, bare har su fitar da anko, domin yanayin da ake ciki na karancin kudi a hannun mutane. Amma a bangaren mata wannan karan za su yi ankon leshi ne fari da Sallah. Shinkafa da miya da kunun zaki kafin aje Sallar Idi zan ci. Matasa da su guji yin budurwa ranar Sallah, domin gujewa rudani nan gaba.