• English
  • Business News
Thursday, June 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara 9 Da Sace ‘Yan Matan Makarantar Chibok

by Leadership Hausa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Shekara 9 Da Sace ‘Yan Matan Makarantar Chibok
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A halin yanzu har an cika shekara 9 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari makarantar sakandire ta ‘yan mata da ke garin Chibok a Jihar Borno inda suka sace tare da yin garkuwa da ‘yan mata 276 daga dakunan kwanansu, daga cikin wadannan ‘yan makaranta har yanzu da akwai sauran ‘yan mata 98 a hannun ‘yan ta’addan.

Sace ‘yan matan makarantar Chibok da aka yi a ranar 14 ga watan Afrilu 2014 shi ne na farko a fadin duniya, inda aka sace tare da yin garkuwa da ‘yan mata masu yawa haka a lokaci daya Kamar yadda aka yi zato lamarin ya dauki hankalin al’umma duniya da shugabanni a bangarori da dama na rayuwar al’umma da suka hada da na siyasa, kasuwanci, wasanni da sauransu inda aka yi kira da nuna bukatar a tabbatar da an ceto su ba tare da wata matsala ba.

  • Ban Da Masaniya Kan Yi Wa Shugaban NIS Jere Ritaya – Aregbesola 
  • Sin Ta Samarwa Kasashen Waje Tallafin Ayyukan Likitanci Ba Tare Da Sharudan Siyasa Ba

Saboda tabbatar da an ceto ‘yan matan ne har aka kaddamar da gangamin tiwita mai suna ‘hashtag, #BringBackOurGirls (#BBOG)’ wanda ya mamaye sassan duniya daga baya aka haifar da wata kakkaffar kungiya mai suna Bring Back Our Gilrs wadanda ‘yan gwagwamarmaya Aisha Yesufu da Hadiza Bala, da tsohuwar ma’aikaciyar Bankin Duniya da kuma Ministar Ilimi, Dakta Oby Ezekwesili suka jagoranta, sun yi watanni suna gabatar da zaman dirshan da zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba don ta zafafa kokarin da take yi na ceto ‘yan matan.

Irin halin ko in kula da gwamnatin Goodluck Jonathan da kuma yadda wasu jami’an gwamnatin suke yi ta nunawa a kan lamarin ‘yan matan Chibok ya sanya al’umma suka kasa gamsuwa da kokarin da gwamnatin take yi na ganin an ceto ‘yan matan, wanda hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sanya Shugaba Jonathan ya kasa lashe zaben hankoronsa na darawa karagar shugabancin Nijeriya karo na biyu a shekarar 2015.

Haka kuma duk da alkawarin da gwamnatin Shugaba Buhari da ta biyo bayan na Jonathan ta yi na ceto yaran ba a cimma nasarar hakan ba har zuwa yanzu. Gwamnatin ta samu nasarar ceto ‘yan mata 100 a lokutta biyu, daban-daban ta hanyar tattauanawa da kuma amfani da salon bani gishiri in baka manda da wadanda suka sace yaran, duk kuwa da cewa, gwamnati ta karyara cewa, an bayar da kudi a yayin karbar ‘yan matan.

Labarai Masu Nasaba

Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis 

Kano Ta Ayyana Ranar Alhamis Hutu Domin Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

A tsawon wannan lokacin wasu ‘yan matan sun samu nasarar tserewa daga wadanda suka sace su ko kuma yayin da aka kashe ‘yan ta’addan da ke rike da su wasu kuma sojoji da jami’an tsaro ne suka ceto su a farmakin da suke kaiwa a yankin arewa maso gabas. Da yawa daga wadanda aka ceto duk sun zama matan aure wasu ma sun haihu, ‘yan ta’addan ne ke aurensu. Gaba daya zuwa yanzu a kwai ‘yan mata 98 da ba a san halin da suke ciki ba zuwa yanzu, duk da kuma ana fargabar cewa, wasu ‘yan matan na iya mutuwa a musayar wuta da ake yi a tsakanin juami’an tsaro da ‘yan ta’adda da kuma wsasu dalilai masu yawa da za su iya kai wa ga mutuwar wasu daga cikin ‘yan matan.

Akwai labari mai kara karfin gwiwa da ke nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan matan da aka ceto sun koma makaranta a cikin gida da wasu ma a wasu kasashen duniya, wasu sun shiga jami’ar ‘American Unibersity of Nigeria (AUN), Yola, a karkashin tallafin karatu na gwamnatin tarayya. A watan Mayu na shekarar 2022, daya daga cikin ‘yan matan mai suna, Lydia Pogu, ta kammala karatun ta na digirin digirgi daga wata jami’ar kasar Amurka, mai suna ’Southeastern Unibersity, USA, yayin da wasu daga cikin su suka kammala digiri daga wasu jami’o’in.

Tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok dubban wasu ‘yan matan a wasu makarantun su fuskanci cin zarafi da dama a lokutta daban-daban tun daga yadda aka sace wasu ‘yan matan a makarantar Dapchi da ke Jihar Yobe a shekarar 2018 zuwa na baya-bayan nan da aka yi ranar 7 ga watan Afrilu 2023, inda ‘yan bindiga suka sace yara 80 a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Hukumar kulawa da al’amura gaggauwa na kanana yara ta bayyana cewa, daga shekarar 2014, an samu cin zarafin yara har sau 2,400 inda abin ya shafi yara fiye da 6,800 a yankin arewa maso gasas, cikin cin zarafin yaran sun hada da yadda ‘yan ta’adda ke shigar da yara kanana harkokin ‘yan bindiga da kuma yadda ake samun labarin sace yara fiye da 693 a ayyukan ta’addanci da aka yi ma fiye da 675 a sassan kasar nan.

Mummunan tasirin ayyukan ta’addan a kan harkar ilimi yana da girman gaske zai kuma ci gaba da samar da matsalar zuwa wani lokaci mai yawa a nan gaba. Hukumar  Kula da Malaman makaranta ‘Teachers’ Registration Council of Nigeria (TCN)’ sun bayyana cewa, sun bayyana cewa a tsakanin shekarar 2009 da 2022, an kashe malamai fiye da 2,295 a hare-haren da aka kai musu an kuma tarwatsa rayuwar malamai 19,000 haka kuma an kulle makarantu 1,500 saboda matsalar tsaro abin da kuma ya kai ga lalata makarantu fiye da 910 a hare-haren ta’addanci da aka kai.

Abn takaici kuma a nna shi ne, yanzu shekara 9 ke nan bayan da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok, amma har yanzu babu alamar za a dakatar da sace-sacen ‘yan makaranta a Nijeriya, yan ta’adda a yankin arewa maso gabas, arewa ta yamma da arewa ta tsakiya na ci gaba da cin karen su babu babbaka, jihohin  Zamfara, Jigawa, Niger, Kaduna da Kebbi na daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ta’addanci a kan makarantu wanda hakan na nuna cewa, shirin nan na gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro a makarantun mu ya sha ruwa kenan.

A ‘yan watannin da suka wuce yayin da ake hada-hadar yakin neman zaben 2023 babu wani magana da aka ji daga masu takara a kan halin da ‘yan matan Chibok ke ciki, yanzu kuma gashi wa’adin gwamnatin Buhari yana gab da karewa babu wata magana na yadda za a ceto sauran ‘yan makarantare Chibok 98 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda da ba a san halin da suke ciki ba. A matsayinmu na gidan jarida muna kira ga gwamnati mai kamawa da ta tabbatar da ta yi tsare-tsaren da zai ga ceto wadannan ‘yan mata don kasance da iyalansu, haka kuma akwai bukatar su samar da tsarin kare makarantu da ‘yan makaranta daga fadawa hannun ‘yan ta’adda.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan Matan ChibokBoko Haram
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ina Neman Gafarar ‘Yan Nijeriya Idan Na Muku Ba Dai-dai Ba —Buhari

Next Post

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattauna Kan Zamanintarwa Irin Ta Sin Da Duniya

Related

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis 

7 hours ago
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu
Manyan Labarai

Kano Ta Ayyana Ranar Alhamis Hutu Domin Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

17 hours ago
Sojoji
Manyan Labarai

DHQ Za Ta Tura Dakaru Na Musamman 800 Yankunan Da Ke Fama Da Rashin Tsaro – CDS

21 hours ago
Gwamnatin APC Ta Kara Ingiza ‘Yan NIjeriya Cikin Bakin Talauci – PDP
Manyan Labarai

PDP Ta Soke Babban Taronta, Ta Dawo Da Anyanwu A Matsayin Sakatarenta

1 day ago
KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano
Manyan Labarai

KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano

1 day ago
Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano
Manyan Labarai

Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano

1 day ago
Next Post
Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattauna Kan Zamanintarwa Irin Ta Sin Da Duniya

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattauna Kan Zamanintarwa Irin Ta Sin Da Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

June 26, 2025
Kawayen amarya

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina

June 26, 2025
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna

Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Bindiga Ta Ci Rayuka Da Dama A Jihar Neja

June 26, 2025
Tinubu

Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis 

June 26, 2025
Cristiano Ronaldo Na Shirin Tsawaita Kwantiraginsa A Kungiyar Al-Nassr

Cristiano Ronaldo Na Shirin Tsawaita Kwantiraginsa A Kungiyar Al-Nassr

June 25, 2025
Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC

Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC

June 25, 2025
Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya

Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya

June 25, 2025
MSS: Neman Sinawa ‘Yan Leken Asiri Da CIA Ta Yi Tamkar Wasan Ban Dariya Ne

MSS: Neman Sinawa ‘Yan Leken Asiri Da CIA Ta Yi Tamkar Wasan Ban Dariya Ne

June 25, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Kano Ta Ayyana Ranar Alhamis Hutu Domin Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

June 25, 2025
Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato

June 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.