Mai fashin baki game da alakar kasa da kasa dan asalin kasar Zimbabwe Gibson Nyikadzino, ya ce shawarar da kasar Sin ta gabatar game da tsaron kasa da kasa ko GSI a takaice, ta ingiza burin da ake da shi na wanzar da zaman lafiya da tsaro, da daidaito, tare da sanya kyakkyawan karsashi ga duniya baki daya.
Nyikadzino, wanda ya zanta da kafar dillancin labarai ta Xinhua, ya ce Sin ta zamo babban jigo a fannin wanzar da zaman lafiya da tsaro, a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubaloli.
A watan Afrilun shekarar 2022 da ta gabata ne kasar Sin ta gabatar da shawarar GSI, wadda ke da nufin samar da sabuwar hanyar wanzar da tsaro, ta hanyar tattaunawa maimakon yin fito-na-fito, da hadin gwiwa maimakon kafa wani gungu, da cimma moriyar juna maimakon salon “wani ya samu wani ya rasa”.
Masanin ya kara da cewa, yayin da manufofin tsaro na kasashen yamma ke mayar da hankali ga amfani da matakan soji wajen shawo kan rigingimu, a daya bangaren Sin ta gabatar da shawarar wanzar da zaman lafiya mai nagarta, wadda za ta ba da gudummawa ga wanzuwar tsaron duniya.
Masanin ya ce ya damu matuka da tasirin manufofin harkokin wajen kasashen yamma, masu ba da karfi ga matakan soji, bisa irin mummunan tasirin da suka yi a kasashe irin su Afghanistan, da Iraki, da Syria da Libya. A cewar sa, irin wadannan manufofi an kirkire su ne da nufin amfanar da kamfanonin kirar makamai, matakin da ya yi matukar illata zaman lafiyan duniya.
Kalaman na Nyikadzino dai sun yi daidai da na masanin tattalin arziki dan kasar ta Zimbabwe Paul Musodza, wanda yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya bayyana shawarar GSI din a matsayin wadda ta bunkasa zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa a duniya baki daya.
Musodza ya kara da cewa, baya ga shawarar GSI, kasar Sin ta kuma gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da shawarar bunkasa ci gaban duniya, da kuma shawarar wayewar kan duniya baki daya.
Daga nan sai ya jinjinawa tasirin shawarwarin na Sin, ganin irin gajiya da kasashen nahiyar Afirka, da ma na sauran sassan duniya za su ci daga gare su. (Saminu Alhassan)