Alhaji Umar Ahmad MD Ahuda ya bayyana cewa akwai bukatar shugaban kasa mai jiran gado, Ahmad Asiwaju Bola Tinibu ya rubayya kokarin Shugaban kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari na bun-kasa harkokin noma.
Ya ce Shugaba Buhari ya kasance na farkon a tarihin Nijeriya wajen zuwa da tsatsare na tallafa wa no-ma, akwai bukatar zababben shugaban kasa ya yi kokari irin na Buhari a wannan fanni, wanda hakan zai tabbatar da ci gaban Nijeriya da kuma al’ummar wajen dogaro da kai da samun abinci.
- Bai Kamata Japan Ta Zuba Ruwan Da Sinadarin Nukiliya Ya Gurbata Cikin Tekun Pasifik Ba
- Rikici Ya Barke Wajen Jana’izar Dan Wasan Da Ya Kashe Kansa
Haka kuma Alhaji Umar ya shawarci wadanda suka nemi mukamai a jam’iyyu daban-daban da ba su samu nasara ba su rungumi kaddara, su tara gaba mulki na Allah ne shi ne mai bayarwa da akasin haka. Ya ce akwai bukatar su mara wa wadanda suka sami nasara baya domin ciyar da kasar nan, hakan zai kawo zaman lafiya da kawar da rigingimu a matakan jihohi da kasa.
Ya hori manoma da sauran al’umma kan su hada kai tare da yin amfani da darusan Azumun watan Ram-adan ta hanyar jaddada imani da tausaya a tsakanin juna.
A karshe ya yaba wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan samar da hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Maradi a Nijar, wacce ta biyo ta Kazaure, Danbatta da sauran garuruwa da jihohin Nijeriya wanda zai kawo ci gaban jama’a a kowani fanni na rayuwar al’ummar kasar nan.