Tsohon dan wasan kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya ce yana son ya nuna wa Manchester United cewar ta yi kuskure da ba ta tsawaita kwantiraginsa ba a ci gaba da zaman kungiyar.
Wasu rahotanni na cewar Manchester United ta yi masa tayin fam 300,000 uku a kowanne mako domin ya ci gaba da buga mata wasa sai dai a wani shirin talbijin kan tarihin dan wasan da ake sayarwa a Amazon mai suna ‘The Pogumentary’, Pogba ya ce duk batun na ‘yaudara’ ne.
Ana sa ran zai sake komawa Jubentus, bayan da ya bar United sakamakon karewar kwantiraginsa a kakar da aka kammala, sannan a shirin talbijin din na Pogba, wanda za a fara nunawa ranar Juma’a, dan wasan ya yi magana kan tsohon wakilinsa, Mino Raiola, wanda ya mutu bayan doguwar jinya a watan Afrilu.
Wani bidiyo da PA news ta gani daga tarihin Pogba ya ce yana son ya nuna wa Manchester United sun yi kuskure da suka ki bashi sabuwar yarjejeniya zai kuma nuna wa sauran kungiyoyi kuskuren da kungiyar ta yi na kin tsawaita zamansa da su.
Rahotanni dai sun bayyana cewa Manchester United ta yi wa Pogba dan Faransa tayin kwantiragi mai tsoka, amma ya ce a bidiyon ‘yaudara ce, sannan ya kara da cewa ta yaya za’a sanar da dan wasa kana bukatarsa, amma ba’a yi masa tayin yarjejeniyar tsawaita zamansa ba.
Pogba, wanda ya fara buga Manchester United a makarantar horon ‘yan wasa matasa daga Le Habre yana da shekara 16 a 2009, an amince ya bar kungiyar a matakin wanda kwantaraginsa ya kare a 2012.
Sannan daga nan ya lashe gasar Serie A guda hudu a Jubentus daga nan ya sake komawa Manchester United kan kudi fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya a watan Agustan 2016.
Shekara biyu tsakani ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya da ta kai Faransa ta lashe kofin a wasannin da Rasha ta karbi bakunci, sannan daga baya dangantaka ta yi tsami tsakanin Pogba da Jose Mourinho, kan rashin kwazonsa a lokacin wasanni da yawan jinya.