ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Yi Wa Masu Garkuwa Kofar Raggo, Suka Kwace AK-47 Da Harsasai A Zamfara

by Sabo Ahmad
4 years ago
'yansanda

‘Yansanda a jihar Zamfara, sun tabbatar da cewa jami’an da aka tura yankin Bukkuyum da Gummi sun kwato bindiga kirar AK-47 da harsasai guda 18 daga wajen ‘yanbindigar a jihar.

Kwamishinn ‘yansandan jihar Mista Ayuba Elkanah, ya ce,rundunar za ta ci gaba da lalubo masu garkuwa a dukkan inda suka boye, domin fatattakarsu da kawo karshensu.

Kwamishinan ya ce,“Ranar 19 Yuli 2022, rundunar ‘yansandan da ke yankin Gummi da Bukkuyum sun samu wani kira, wanda ake sanar da su cewa,wasau masu garkuwa a kan babur sun dira a Saran Gamawa da Unguwar Mata da niyyar kashe mutane da kuma kama wasu domin yin garkuwa da su.

ADVERTISEMENT

Saboda haka, rundunar ‘yansanda da hadin gwiwar ‘yansintiri na wannan yankin suka hadu, don yin fito-na-fito da ‘yanbindigar.

“Sakamakon haka an yi wa daya daga cikin masu garkuwar mummunan rauni, tare da kwace bindiga kirar AK-47 da kuma wasu kwanson alburusai,”in ji shi.
Elkanah ya yaba da yadda jami’an tsaron na hadin gwiwa suka gudanar da aiki kafada da kafada da kuma samun nasarar da suka yi.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Kwamishinan ya kara da cewa, yanzu haka, ya umarci rundunar ‘yansandan da ke Anka da DPO din da ke yankin da su kara wa ‘yansandan da ke zagaye karfi, yadda za su iya fuskantar dukkan wasu masu aikata miyagun laifukan da ke wannan yanki.

Rundunar, ta tabbatar wa da al’ummar wannan yankin cewa, za ta ba su kariya ta musamman. A karshe, ya yi kira da babbar murya ga al’ummar wannan yanki da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin ganin an samu nasara a harkar tsaron.

'yansanda
Sabo Ahmad
+ postsBio
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    An Gurfanar Da Mutum 3 Bisa Laifin Lakada Wa Wani Duka Har Lahira
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Uwa Ta Mutu A Kokarin Raba Fada Tsakanin ‘Ya’yanta A Abuja
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    ’Yan Fashi Sun Yi Shigar Injiniyoyi, Sun Saci Manyan Na’urorin Sadarwa

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
NNPP

NNPP Ta Kaddamar Da Kwamitin Sulhu Da Zaman Lafiya A Neja

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.