Ga duk wani mutum da ke fagen siyasar Kano, daga jamhuriyar siyasa ta biyu (1979 zuwa 1984) har a dangana da wannan jamhuriyar siyasa ta hudu da muke ciki (1999 zuwa lokacin wannan rubutu 2022), babu shakka zai san Rabi Shehu Sharada, koko, zai samu labarinta.
Sai dai, maganar gaskiya, wannan hamshakiyar ‘Yar siyasar ta Kano, an fi sanin ta ne cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu, wanda hakan ba ya rasa nasaba da irin yadda gidajen rediyo musamman na Kano, suka kirkiri dandamalolin siyasa a gidajen nasu, tare da bai wa ‘Yan siyasar ta Kano damar baje kolinsu.
Gidan Rediyo na Firidom da ke a unguwar Sharada, Kano, sune a kan gaba wajen kirkirar irin wadancan filayen baje koli na siyasa, sa’adda suka kirkiri filin Siyasar “Kowane Gauta”, wanda ya fara gudana tsawon lokaci karkashin jagorancin hazikin danjarida Suleman Gama.
Mutane irinsu Ali Baba Fagge, Bashir Jentile, marigayi Shehu Mai Salati Indabawa, Binta Saiyadi, Rabi Sharada da makamantansu, su ne suka kasance a sawun gaba, wajen baje hajarsu ta siyasa a wancan bigire ko fili na Kowane Gauta. Da farko, sunan wadannan ‘Yan gwagwarmayar siyasa da ke magana a filin na Kowane Gauta shi ne “‘Yan Gauta”. Daga baya ne ake kiran masu irin gwagwarmayarsu da “Sojojin Baka” a Kano.
Tun daga jamhuriya ta biyu zuwa yau din nan (1979 –2022), Hajiya Rabi Shehu Sharada, ba ta da wani ubangida na siyasa sai Ambasada Aminu Bashir Wali.
Ba ta ta6a canja ubangidanta na siyasa ba, sanin kowane cewa, irin wannan doguwar biyaiya ta siyasa da Rabi Sharada ta yi wa Aminu Wali ta kusa tsawon Shekaru arba’in (40), ba safai ne ake ganin haka ba tattare da dubban daruruwan ‘Yan siyasar wannan lokaci.
Cikin filin siyasar ta Kowane Gauta da aka kirkira a nan Kano na gidan Rediyon na Firidom, a kowane lokaci ka kunna, Rabi Sharada ba ta komai cikinsa, face kare akidar gidan Ambasada Aminu Wali, sai dai idan ba ta zo ba.
Rabi Sharada dai haifaffiyar cikin birnin Kano ce, yanzu haka tana da Shekaru 57 a Duniya.
Daga Gwagwarmayar Siyasarta
Tun daga jamhuriyar siyasa ta biyu ne, Hajiya Sharada ke bin jam’iyya da kuma akidar gidan NPN Aminci. Sanin kowane cewa, akidun gidajen siyasar Kano tun daga jamhuriyar farko zuwa ta biyu, sun ginu ne akan gidan Nepu da NPC, wadanda a jamhuriya ta biyu su ka rikide zuwa NPN da PRP. Sai dai, daga jamhuriya ta biyun, zuwa wannan ta hudu da muke ciki, gidajen akidun siyasar, maimakon biyu, sun rikide ne zuwa uku, sune, Santsi da Ta6o da kuma gidan NPN.
Tun daga wancan lokaci zuwa yau, Hajiya Sharada ba ta sauya gidan siyasarta na NPN ba, kuma a gidan ba ta da ubangida sama da Aminu Wali. Ko ba komai, cikin gwagwarmayar wannan baiwar Allah, za a fahimci jajurcewa, kaifi-daya da alkawari tattare da ita.
Hajiya Rabi Shehu Sharada ba ta kasance mai tsoro ba cikin kare akidar siyasar gidan da ta yi imani da shi, ko da kuwa hakan zai kai ga ta rasa rayuwarta ne kacokan.
An sha kama ta a kulle, an zazzage ta ya fi sau shurin-masaki, an sha bugunta daga lokaci zuwa lokaci, duk dai a kan hanyarta ta kare mutunci da akidar gidan siyasarta na NPN, uwa-uba, da kuma kare irli da muhibbar maigidanta na siyasa, wato Ambasada Aminu Bashir Wali. Da yawa daga ‘Yan’uwan Rabi da ‘Ya’Yanta, na kyamar irin kafiyar da take da, a fagen na siyasa, wanda ke jawo mata bugu da dauri da kuma cin-mutunci dare da rana.
Sai dai a kullum, ta kan ba su hakuri ne, tare da fadakar da su tarihin wasu zakwakuran mata ‘Yan siyasa da aka yi cikin arewacin wannan Kasa, irinsu Asabe Reza, Gambo Sawaba da makamantansu, wadanda suka jajurce kai-da-fata sai talaka ya ji dadi karkashin mulkin Dimukradiyya a Kasar. Tilas dole ne ‘Yan’uwan nata ke hakura, amma ba don sun gamsu ba.
Manyan ‘Yan Siyasar Kano Na Zawarcin Rabi Sharada
Babu wasu manyan mutane a Kano karkashin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu, da za a ce ba su yi zawarcin Hajiya Rabi Shehu Sharada ba, na ta koma gidan siyasarsu, ta bar Aminu Wali da kayansa na NPN, amma ina! Sai dai a ga ta yi watsi da irin wancan goron gaiyata na siyasa da ake ta faman kai mata dare da rana dodo-dodo.
Duk da irin galla na wadaka da warisa da aka yi karkashin gwamnatin Malam Shekarau a Kano na tsawon Shekaru 8, anyi-anyi da Rabi ta koma cikin daular gwamnatin ANPP, amma ta ki, duba da cewa, maigida Aminu Wali na cikin jam’iyyar PDP ne a lokacin, saboda haka, kafarta kafarsa.
Duk wata shahara ko daukaka da mutum zai nema karkashin inuwar jamhuriyar siyasa, gwargwado za a iya cewa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso ya same ta.
Ya yi Ministan Tsaro na Shekaru 4, ya yi Ambasada, ya yi gwamna na Shekaru 8 a Kano da sauran wasu mukamai ma da ya rike gabanin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu. Amma duk da irin wannan daukaka ta Kwankwason, ya zauna har sau biyar (5) da Rabi Sharada, yana mai roko da godon ta dawo cikin tafiyarsa ta siyasa, amma ta ki yarda. Ita dai a kullum aka ta6a ta, “Sai Wali, Sai Wali” shi ne amsar da take bayarwa. Ta labartawa wannan mai rubutu da bakinta cewa, a zamanta na karshe da Sen. Kwankwaso, ganin ta ki aminta ta je cikin tawagarsa ta siyasa, tashi ya yi daga zaman nasu, cikin fushi ya ce da ita “…To ba sai ki je ki shirya tsakanina da Walin ba…”. Sai take cewa da shi, “Wace ni!, na yi kadan da na ce zan shirya ka da shi”. Ta cigaba da fada cewa, har ta yin mukami Kwankwason yake mata, amma ita a kullum gunkin siyasarta shi ne Aminu Wali.
A kullum, Hajiya Rabi Shehu Sharada, wanda take kallo a matsayin uwa-uba nata na siyasa shi ne dai Aminu Wali. Da bakinta ta fadawa mai yin wannan rubutu cewa, “Ni fa Aminu Wali kallon ubana nake masa a rayuwata…” (Sai dai ta nuna a da ne take yi masa irin wannan kallo). Hajiya Rabi, ba ta ta6a yin tafiyar siyasa ba a karkashin duk wani mahaluki madaukaki da mai karatu ya sani cikin siyasar Kano, face dai Ambasada Aminu Bashir Wali.
Sharada, ba ta6a yin tafiyar siyasa karkashin Kwankwaso ko Shekarau ko Ganduje ba. Hatta ma wasu dake siyasa da suka zo bayan wadannan bajiman mutane uku, sun nemi Rabi Sharada da ta zo su yi tafiyar siyasa, amma ta yi bulun-bukwi, cikinsu har da Mohammed Abacha, ya yi-ya yi ta zo su yi tafiyar siyasa, amma amsarta ta shekaranjiya da jiya, ita ce ma dai a yau take bayarwa, ma’ana sai Wali!
An Ci Moriyar Ganga An Yasar Da Kwaurenta
Mai karatu ba zai fahimci matashiyar wannan rubutu ba, sai idan an labarta masa hali da kuma yanayi na matsananciyar rashin lafiya da a yau Hajiya Rabi Shehu Sharada ta tsinci kanta ciki. Bugu da kari, izuwa karshen wannan labari, zai yi kyau mutanen da ke yin salon siyasar ko-a-mutu ko a yi rai, saboda wani mutum can, lalle-lalle ne su shiga taitayinsu, su sani cewa fa Annabi ya faku, tare da mayar da irin makauniyar soyaiyarsu zuwa ga Allah da ManzonSa kadai, amma ba waninsu ba.
Ganawata Da Hajiya Rabi Shehu Sharada
Mai wannan rubutu bai faye son kifuwa bisa batutuwan da ke yawo a teburan masu shayi cikin birni da karkara ba, ko irin wadanda ake samu a kan dakalin mati. Abin nufi, a kullum mai wannan rubutu, yana mayar da hankali wajen gabatar da batutuwa masu alfanu ga al’uma, wadanda su ka fito daga bakunan masana, daga majiyoyi masu tushe.
Haka batun yake ga duk mai nazartar rubuce-rubucensa. Wannan dalili ne ya ja shi zuwa ga ganewa idanunsa irin mugun yanayi na ban-tausai, da ya ji a na yamadidinsu a gari, cewa, wai, Rabin na cikin mummunan yanayin rashin lafiya, kuma abu mafi munin ji shi ne, wai maigidanta na siyasa Aminu Wali, ya nuna halin ko-in-kula da yanayin da sahabiyarsa Sharada ke ciki.
Ranar Alhamis Ne Na Yi Kwalli Da Rabi Sharada—16 ga Yuni, 2022
Don gudun furta wani abu da mutum zai yi nadamar fadi a karshe, don taimakon Rabi Shehu Sharada, idan abinda ake fadi gaskiya ne, don zuwa daukar darasin rayuwa, don ankarar da mutane abinda akasarinsu ke gaza ganewa cikin siyasar yau, don adana hujja ga masu bincike gami da yin adalci ga tarihi, sune daga dalilan da suka fizge ni zuwa ga yin kwalli da mara lafiya Sharada.
Bayan karfe 12 na rana ne na isa gidan nata, wanda ke a unguwar Sharada, Kano, can kasa, bayan babban Masallacin Juma’a na Sharada.
Bayan na yi sallama, an yi min iso izuwa ciki, na ma sami tsohon kakakin hukumar ‘Yan sanda ta jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya, a ciki. Ya zo ya duba ta, shi da wani, ko dai abokinsa ne ko kuma yaronsa. Muka gaisa cikin mutuntawa. Ya gabatar min da kansa. Bugu da kari, na yi kwalli ma da wasu ‘Yan dubu dubun da ba su gaza 5 zuwa 10 ba a gefenta, wanda nake tunanin su ne suka agaza mata da su, kudin-dubiya.
Canjin Yanayi Na Bugawa
Ba na son fito da ma’anar canjin yanayi na bugawa a cikin runfar da Hajiya Rabin ke zaune, bisa wata kujera mai cin mutane uku, kafa daya a bisa kujerar, gudar kuma, na kasa, tana mai fuskantar bangaren arewa na runfar tata. Babu shakka, sai mutum ya yi da gaske ne zai iya yin zaman minti 3 a runfar, saboda wancan canjin yanayi da ke bugawa. Sai na fara yin wani tunani cewa, ‘Yanzu wannan ce wannan ‘Yar kwalliyar da ba ta rabo da turare, Hajiya Rabi Shehu Sharada, ita ce ‘Yar kasuwar nan mai rufin asiri da ake fadi ko kuwa?…”.
Shigata ke da wuya ne ASP Majiya da abokin tafiyarsa su ka fice, a fuskar abokin tafiyar tasa, akwai takunkumin fuska, Wallahi cikin raina, na yi burin, inama ni ma na zo da nawa takunkumin fuskar. Sai ya zamana, daga ni cikin runfar, sai Rabi da kuma wata mata, ga dukkan alamu kawarta ce. Minti 2 minti 3, sai ka ga Rabin na zub da hawaye a fuskarta, ko me yasa oho? Sai dai matar da suke tare, na ta lallashinta ne.
Na gabatar da kaina ne a matsayin wanda ke yin rubuce-rubucen siyasa, wallafa littafi da yin rubutu a jarida. Jin yanayin da take ciki, da abubuwan daure-kai da nake yawan ji game da ita dare da rana, sune suka ja hankalina zuwa ga jin gaskiyar lamari daga bakinta, tare da tunanin, ta ina ne nake ganin zan iya taimakonta.
Tun da wannan marubuci yake a Duniya, bai ta6a yin magana ko da ta minti guda ne ba da Hajiya Rabi Shehu Sharada ba, sai a wannan rana ta Alhamis. Ta matukar ji dadin bayanina, ta yi na’am. Ta kara da cewa, babu wani danjarida da ya zo gida ya same ta.
Ciwon Dake Addabar Rabi Shehu Sharada
Abin tausayi, Hajiya Rabi a yau, na fama ne da matsanancin ciwon kansar mama “Breast Cancer”, har ta kai ma ga an yanke mamanta na 6arin hannun dama.
Yadda take labartawa shi ne, ciwo ne da ya rika tafiya yana dawowa. An yi ta fama da shi ne a farkon lamari a tsaitsaye.
Ciwon dajin, ya kere Shekaru biyar tana fama da shi, amma bai kai ta kasa wanwar ba, sai Shekaru biyu da suka gabata. Daga lokacin ne zuwa yau, komai nata, harkokin siyasa, kasuwanci da makamantansu suka tsaya cik. Lokacin da aka shiga matsanancin yanayin cutar Korona, sai ya zamana ta sami bizar fita Kasar Indiya don yin magani, amma sai aka wayigari an dode iyakokin Kasashen Duniya. Daga wancan lokaci fa zuwa yau, sai dandanar mugun radadin ciwon ne take yi, tare da yin magani cikin yanayi na yau akwai, gobe babu.
“Komai Nawa Ya Kare Karkaf”
Hajiya Rabi ta cigaba da cewa, shi maganin wannan cuta ta kansa, na mugun cin kudade ne. Ba abin mamaki ba ne a rubutowa mutum maganin dubu hamsin, dubu dari, koma sama da haka a lokaci guda.
Bugu da kari, akan ja kunnen mutum cewa, lalle ne ya je manyan shagunan sayar da magani irinsu Well Care da makamantansu, bisa hujjar cewa, a can ne ake samun gangariyar magungunan da lokacin amfaninsu bai kare ba, kuma a cikinsu ne ake sanyawa magungunan na’urar sanyaya waje. Haka ta rika kai gwauro tana kai wa mari tsakanin irin wadannan manyan shaguna da kudinka ne kawai zai ba da damar a kula ka.
Akalla Rashin Lafiyar Ta Lashe Kudi Naira Miliyan Shida (#6,000,000.00)
Baiwar Allah Sharada, ta yi karin hasken cewa, wannan rashin lafiya da take ciki, ta lashe zunzurutun mazajen kudade akalla naira miliyan shida zuwa sama. Ba ya ga sayen irin wadancan magunguna masu shegiyar tsada, shi ma wankin ciwon da ake yi a asibiti kusan kullum kwanan Duniya, ya lankwame tarin kudade masu yawa : da farkon fara wankin, ya fara ne da naira dubu kullum, daga baya farashin ya tashi. Zuwa yanzu, an dauki kimanin Shekaru biyu ke nan ina zuwa wankin ciwon.
Ni mutum ce mai neman na kanta, ina yin harkokina na kasuwanci, amma yanzu haka duka jarina ya lume cikin wannan rashin lafiya da nake fama da ita (tana bayani, tana zub da hawaye akai akai. Ita ma daya matar dake kui6inta na share nata hawaye da gefen gyautonta).
Ba ya ga gurbin ciwon Sharada da za a ganshi danyen nama ca6e da jini, sai ya zamana kuma daukacin 6arin jikin nata na dama da aka yanke nonon, shi ma ya kumbura suntum, musamman hannun nata na dama.
Ta cigaba da fada min cewa, a kullum da safe, da zarar ta tashi daga barci, sai ta ga daukacin jikinta ya kumbura suntum, a hankali a hankali ne za ta ga ta ya fara sacewa. Na ma same ta ne a sace lokacin da na je, amma wancan hannu nata na dama, bangaren inda aka yanke maman, ya kumbura, ya ninka girmansa kusan sau biyu. Yayinda nake ganawa da Rabin, na lura cewa, a duk sa’adda fuskarta ke zub da hawaye, sai waccan mata da na same su tare, ta rika lallashinta, tana cewa da ita, “Ki yi hakuri, komai na Allah ne, Allah Ya ba ki lafiya”.
Wani abu da Rabi Sharada ta fada wanda ya daga mini hankali shi ne, cikin Satin da ya gabata, an rubuta mata wasu gwaje-gwaje a asibiti, na misalin naira dubu 50, amma da ranar gwajin ta zo, sai ya zamana kudin bai cika ba. Haka su ka je asibitin, amma su ka dawo gida ba tare da an yi gwajin ba, ta cigaba da kumbura kamar yadda jikinta ya saba yi dare da rana.
Babu shakka dole ne mutum ya rasa ta cewa, idan ya saurari kalamanta, ya ji irin yanayin radadin rashin lafiya da take ciki a yau. Sannan, duk da irin wadancan makudan kudaden da rashin lafiyar tata ta lashe, halin da take ciki a yau na larurar, ya fi duk lokutan baya da suka shude bukatar a taimaka mata. A duk sa’adda mutum ya je ya duba ta a yau, zai ji ne a zuciyarsa cewa, ba lalle ne ma ta kwana da rai ba. Sannan, kai da ka je ka duba tan, idan ka yi mata cikakken sani a da, musamman a fagen siyasa, za ka fara tunanin cewa, ashe shahararrun ‘yan siyasa irinta, masu iyayen gida na siyasa, da suka isa magana hatta a kasashen Duniya, na fuskantar irin wannan dagulewar lamuran da hatta kudaden yin gwaje-gwaje a asibiti ya gagare su?.
Duba da sanin irin dangantaka da Hajiya Rabi ke da shi tsakaninta da manya kuma jiga-jigan ‘yan siyasa a Kano, nan take sai nake tambayarta cewa, to wai Hajiya Rabi, wace irin gudunmuwa manyan ‘yan siyasarmu na Kano su ka ba ki, game da wannan hali na rashin lafiya da kike ciki?. Bayan yin dogon numfashi, sai ga idanunta sun fara yin zubar hawaye, a nan, ni ma na yi kokarin hakurkurtar da ita, tare da nuna mata cewa, ciwo daban, mutuwa daban. Sannan, babu wani ciwo a ban-kasa da ya gagari Allah Ya warkar da shi. Sai na ga ta dan sami kwarin-gwiwar amsa tambayata.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa cikin yardar Allah