Gwamnatocin Sin da Zambia, sun gudanar da bikin cika shekaru 60 da isar tawagar farko ta likitocin Sin nahiyar Afirka, inda suka fara sauka kasar Aljeriya, da kuma bikin cika shekaru 45 da kulla hadin gwiwar Sin da Zambia a fannin kiwon lafiya.
Taron na jiya Litinin dai ya hallara jakadan Sin a Zambia Du Xiaohui, da ministar lafiyar Zambia Sylvia Masebo, an kuma yi amfani da taron wajen yin ban kwana da tawagar likitocin Sin ta 23, da maraba da zuwan tawaga ta 24, da ma maraba da zuwan tawaga ta 26, ta kwararrun likitoci sojoji na kasar, wadanda su ma za su yi aiki a kasar ta Zambia.
Har ila yau, an yi amfani da bikin, wajen sanya hannu kan yarjejeniyar bayar da tallafin kayayyakin aiki na zamani da ake amfani da su a fannin kiwon kafiya, da sauran kayan aikin jinya, ga asibitin koyarwa na jami’ar Levy Mwanawasa dake kasar. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp