Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta kama wasu da ake zargi da aikata daba ta hanyar amfani da wukake suna gallaza wa mutane a birnin Kano.
A cewar bayanai daga wajen wadanda ayyukan ‘yan daban ya shafa, sun ce mutanen da ake tuhuma kan yi amfani da tituna masu cunkoso da wuraren taron jama’a don aikata ta’asar.
- APC Ta Kori Dan Takarar Gwamna Da Zababben Sanata A Jihar Taraba
- Basarake Ya Mutu A Hannun ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Shi A Kogi
Duk da matsalar rashin tsaro, Kano ta kasance cikin kwanciyar hankali har sai da aka samu gungun masu rike da wukake.
An ruwaito cewa ayyukan ‘yan daban ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bayan far musu da bata garin suka yi, yayin da wadanda suka samu tsira kuma ke gamuwa da munanan raunuka.
’Yan daban wadanda rundunar ‘yansandan ta Anti-Daba ta kama – sun yi kaurin suna wajen amfani da wurare masu cunkoso don cin zarafin jama’a da rana tsaka.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa rundunar wajen gano sauran ‘yan kungiyar da ke cikin kwaryar birnin Kano.