Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur a karshen gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a lokacin da ta ke zanta wa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron hukumar da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Mata 2 Sun Mutu A Wajen Hakar Ma’adanai A Bauchi
- Gwamnan Gombe Ya Nada Mai Rikon Safiyo-Janar Da Babban Jami’in Kididdiga
A cewar ministan, hukumar ta kammala taronta da cewa bai dace a dauki matakin ba.
Ta bayyana cewa majalisar ta tattauna kan lamarin kuma ta yanke shawarar cewa ba za a iya cire shi ba a yanzu, amma kuma ta amince da bukatar ci gaba da tattaunawa kan lamarin da kuma aikin share fage tare da hadin gwiwar jihohi da wakilan gwamnati mai zuwa.
Tun da fari shugaba Buhari ya amince da cire tallafin man fetur.
Buhari ya ce tallafin yana wawure maduden kudade duk shekara, wanda hakan ke hana yin manyan ayyuka ga ‘yan kasa.