Mutane shida ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon fashewar wata motar dakon mai da ta kama da wuta a kusa da titin Bauchi kusa da Jami’ar Jos, a babban birnin Jihar Filato.
Baya ga haka, wannan ci gaban ya haifar da firgici a tsakanin al’ummar yankin Jami’ar yayin da aka ga dalibai da masu wucewa suna ta zage-zage don gujewa fadawa cikin rudanin da ya biyo baya.
- Zaben Adamawa: A Hukunta Kwamishinan Zaben Adamawa -Fintiri
- Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci: Kotu Ta Hana Belin Tukur Mamu
Mummunan hatsarin ya yi sanadin mutuwar masu ababen hawa da masu wucewa tare da jikkata wasu da dama a unguwar da ake hada-hada a kan titin Bauchi a garin Jos.
Wani ganau ya shaida wa LEADERSHIP cewa an tsinto gawarwaki kusan shida daga wurin.
Sai dai har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka jikkata ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A halin da ake ciki, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Filato, Caleb Bitrus, ya tabbatar wa LEADERSHIP afkuwar lamarin, sai dai ya ce hukumar ba za ta iya kashe gobarar ba saboda manyan motocinsu na wajen gyara.