‘Yan sanda a birnin Turin na kasar Italiya sun sanar da cewar sun ci tara da dakatar da magoya bayan Juventus mutum 177, bisa kalaman batancin da aka yi wa dan wasa Romelu Lukaku.
An yi wa dan wasan Inter Milan kalaman batanci da cin zarafi ranar 4 ga watan Afirilu a karawar daf da karshe a Copa Italiya da Juventus bayan da kungiyoyi biyun suka tashi 1-1 a wasan farko a Copa Italiya da suka fafata na kakar nan.
A wani jawabi da ‘yan sandan suka fitar, ba su fayyace kwanakin da suka dakatar da ‘yan kallon ba da kuma yawan kudin tarar da suka ce sun yi ba amma kwana daya tsakani da tashi daga karawar, hukumar kwallon kwallon kafar Italiya ta bukaci a rufe wani sashen filin Juventus, wajen da aka fi yi wa Lukaku kalaman batancin da cin zarafi.
Tun farko an dakatar da Lukaku wasa daya, bayan da aka yi masa jan kati a karawar, wanda ya karbi kati biyu na gargadi sai na biyun shine wanda ya je gaban magoya bayan Juventus ya dauki yatsa daya ya dora a kan lebensa, dalilin da aka bashi katin gargadi, sannan aka kore shi.
Daga baya aka soke jan katin da aka bai wa Lukaku, wanda hakan ne yasa dan wasan dan kasar Belgium ya buga wasa na biyu da Juventus ranar Laraba a Copa Italiya na bana.