Rundunar tsaron farin kaya ta (NSCDC) a Jihar Nasarawa ta kama wani mai suna Ibrahim Hashimu mai shekaru 18 bisa zargin lalata da karamar yarinya mai shekaru 4 da haihuwa.
Kakakin hukumar NSCDC, DSC Jerry Victor ne, ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da manema labarai a ranar Juma’a a garin Lafiya.
- Zaben Shugabannin Majalisa Ta 10: Ko Tarihi Zai Maimaita Kansa?
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi A Zamfara
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Afrilu, 2023 a Angwan Magaji, kusa da fadar Sarkin Lafia.
Acewarsa, an ga waddda abin ya shafa na kuka da sannan tana zubar da jini a jikinta.
An ruwaito ta bayyana wa mahaifiyarta yadda lamarin ya faru.
Kakakin ya kara da cewa da samun wannan labari nan take rundunar ta dauki matakin gaggauwa kuma ana cikin haka ne aka kama wanda ake zargin Ibrahim Hashimu aka kai ofishin NSCDC domin amsa tambayoyi.
Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin kuma ya roki a yi masa afuwa.
A halin da ake ciki kuma, rundunar da ke yaki da barna a jihar tare da ‘yan sandan Nasarawa Eggon, sun cafke wasu ‘yan ta’adda guda uku da ake zargi da lalata igiyar wutar lantarki mai karfin 33kV a tashar Mada da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon.
Mutanen ukun da aka kama sun hada da Yakubu Ossan mai shekaru 55 da Mustapha Ibrahim mai shekaru 24 da kuma Hussain Yakubu dan shekara 21.
Rundunar ‘yansandan ta kuma ce ta kama Aisha Saidu ‘yar shekara 22 bisa rahotannin da ta ke cewa ta ci zarafin ‘ya’yanta a garin Lafia babban birnin jihar.
“An ga raunuka a ko ina a jikin wadanda abin ya shafa da aka garzaya da su wurin likita don kula da lafiyarsu,” in ji kakakin.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike bayan haka za a gurfanar da wadanda ake zargin.
Kwamandan NSCDC, Abbas Bappa Muhammed, a lokacin da yake kokawa kan yadda ake lalata kananan yara, fyade a jihar, ya ce hakki ne kan kowa na kars yara mata, yana mai kira ga al’ummar jihar da iyaye da su sanya ido sosai kan yaransu.