Dakarun Bataliya ta 151 ta Operation Hadin Kai, sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram da ba a tantance adadinsu ba tare da ceto wasu ma’aikatan jin kai guda biyu a dajin Sambisa.
LEADERSHIP ta tattaro cewa an kashe ‘yan ta’addan ne bayan da sojojin tare da hadin guiwar rundunar hadin guiwa ta Civilian Task Force da Hybrid Forces inda suka kai farmaki maboyar ‘yan ta’addan a Gargash da ke yankin karamar hukumar Bama a jihar Borno.
A yayin farmakin, ‘yan ta’adda a kalla 135 tare da iyalansu suka mika wuya ga sojoji daga sassan dajin Sambisa daban-daban.
Rahotannin sirri da aka samu daga majiya mai tushe daga Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun boye a yankin ne suna shirin kai farmaki yankin Banki kafin a tarwatsa su.
Majiyoyin sun ce a dalilin wannan hadakar an ceto wasu ma’aikatan jin kai biyu da aka sace daga Monguno a shekarar 2022.
Sojojin sun kuma kwato wasu motoci kirar hilux guda uku tare da daya daga cikin su dauke da bindigar harbo jirgin sama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp