‘Yan uwan sarkin sun sanar da rasuwar babban basaraken gargajiya na karamar hukumar Obudu a Jihar Kuros Riba, mai martaba Joseph Davies-Agba a hukumance.
An bayyana rasuwar Davies-Agba a cikin wata sanarwa da dansa, Mista Kjay Jedy-Agba, ya fitar ranar Lahadi a Kalaba.
- Sojoji Sun Kubutar Da Ma’aikatan Jin Kai 2 Yayin Wani Samame A Dajin Sambisa
- Har Yanzu Wasu Na Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Mutanen Banza —Auwal West
“Daga cikin zuciyata nake sanar da ku rasuwar mahaifina abin kaunata, Mai Martaba, Joseph Davies-Agba, OON, “Uti Item III nq Utugwang, Uti Ukani I na Obudu, Basarake kuma Shugaban Jami’ar Jihar Kuros Riba.
“Ya fara sarautar gargajiya ne shekaru 64 da suka gabata, wanda hakan ya sa ya zama mafi dadewar sarkin gargajiya a Afirka.
“Mu, dangi na kusa, mai yiwuwa ba mu da cikakken bayani game da ka’idar jana’izarsa ta karshe idan aka yi la’akari da matsayinsa na sarki.
Sanarwar ta ce “An tilasta mana bin al’adar mutanenmu a cikin dukkan al’amuran da za su kai ga cikar al’amuransa na karshe,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa za su ji cikakken bayani game da jana’izar da zarar cibiyar gargajiya ta kammala shirinta.
Sanarwar ta kara da cewa “Kamar yadda wannan lokaci da muke ciki, fatana shi ne zukatanku su kasance tare da mu cikin addu’o’i.”