Kwamandan kungiyar da ke yaki da ‘yan sara-suka na Jihar Zamfara, Bello Bakyasuwa, ya tsallake harin ‘yan bindiga a lokacin da yake kan hanyarsa zuwa Jihar Kaduna daga Gusau, babban birinin jihar Zamfara.
A cikin sanarwar da aka sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a yau Talata, Bakyasuwa ya bayyana cewa, ‘yan bindigar dauke da muggan makamai, sun kai masa harin a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya da maraicen ranar Alhamis din da ta gabata.
- Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 154 A Nijeriya —NCDC
- Ranar Ma’aikata: NLC Ta Bukaci Daidaita Albashin Ma’aikata A Kebbi
Bakyasuwa wanda tsohon soja ne, ya ci gaba da cewa, “Na tsallake harin ‘yan bindigar kwanaki hudu lokacin ina kan hanyar Kaduna zuwa Funtua daga Zariya.”
Ya kara da cewa, “A yanzu haka, ina kwace a gadon asibiti, rayuwata na cikin hatsari, ina fuskantar yawan kai min hari da nake zargin wasu ‘yan bindiga ne, ke daukar nauyi. ”
Bakyasuwa ya kuma jaddada cewa, harin ya auku a kan sa ne, lokacin da yake kan hanyarsa daga Gusau zuwa Kaduna a cikin motarsa kirar Hilux, inda ya ce, ya lura da wasu motocin Hilux biyu da kuma wata motar kirar BMW na binsa a baya.
Kwamandan ya bayyana cewa, “Ganin cewa, hankali ba bai nutsu da motocin da ke bina a baya ba, sai na tsaya a wajen duba ababen hawa da ke a Yankara, inda motocin suka wuce.”
A cewarsa, “Daga nan, na ci gaba da tafiyata bayan na wuce garin Funtua da misalin karfe 8:30 na daren ranar, na lura da mota kirar Hilux da mota kirar BMW na bi na a baya, inda motar ta BMW ta shiga gabana ta kuma tilasta min tsayawa akan hanyar.”
Ya bayyana cewa,” Wadanda ke a cikin motar sai kwai suka fara bude wa motar da nake ciki wuta, inda muka shafe awanni muna yin musayar wuta da su. ”
Ya ce, “Na yi tsalle daga cikin mota ta, inda hakan ya janyo na samu raunuka a fuskata na kuma yi targade a kafata.”
Bakyasuwa ya ci gaba da cewa, ”’Yan bindigar wadanda aka yo hayarsu sun ci gaba da harbi, amma na samu nasarar tsallake wa na shiga wani daji jini na zuba daga jikina.”
Ya ce, ya ci sa a ‘yansanda sun iso wajen bayan sun ji harbin bindiga, inda suka yi gaggawar kubutar da ni suka kuma kaini asibiti.
Ya ce, “Bayan an duba ni a asibitin na kwana a kauyen da safe direbana ya zo kauyen ya sauke ni zuwa Kaduna don a duba lafiyata sosai. ”
Bakyasuwa ya bayyana cewa, motarsa ta lalace sosai biyo bayan ta sha ruwan albarusai, inda ya koka da cewa, ko a ‘yan watannin baya, wasu ‘yan bindiga sun kai wa direbansa hari a garin Gusau lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa unguwar Gwaza zuwa Gusau, inda suka kwace motarsa.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kawo masa dauki, domin rayuwarsa na a cikin hatsari.