Kwatsam ba zato ba tsammani, wani sojan kasar Uganda da ke aikin bada kariya ga ministan karamin ministan kwadagon kasar Kanal Charles Okello Engola (mai ritaya) ya bude masa wutan harsasai daga bisa kuma sojan ya kashe kansa da kansa.
Rahotonni da suka zo mana sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata a gidan ministan da ke Kampala babban birnin kasar.
- Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 154 A Nijeriya —NCDC
- Motar Da Ta Kwaso Daliban Nijeriya Daga Sudan Ta Kama Da Wuta
Kodayake ba a samu wani bayanin da ke nuni da cewa ko wani sabani ko rashin fahimta ne ya shiga tsakanin sojan da ubangidansa ba.
Wadanda lamarin ya faru a kan idonsu sun shaida cewar bayan da sojan ya harbe mai gidansa, ya cigaba da harbin kan mai uwa da wabi musamman harbi a sama yayin da ya jikkata wasu da dama kana daga karshe ya juya bindigar a kansa kuma ya mutum.
Bidiyoyin da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka taru a wajen da lamarin ya faru cikin alhini.