Rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da hadin guiwar ‘yan sandan kasar Hungary sun hada kai domin cafke wani matashi dan shekara 21 da ake zargi da damfara ta yanar gizo.
Wanda ake zargin, George Gift Ikata, dan shekara 21, dan asalin karamar hukumar Abua ta jihar Ribas, an kama shi ne da laifin kirkirar wata manhajar yanar gizo wacce ake amfani da ita wajen damfarar ‘yan kasashen waje musamman ‘yan kasar Hungary.
Kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, “Rundunar ta samu sako daga rundunar ‘yan sandan kasar Hungary a ranar 15 ga Yuli, 2022. Cewa akwai wani shafin yanar gizo da ake zargin na damfara ne mai suna ‘AMC Stock Experts’, shafin ya yi nasarar damfarar wasu masu kasuwancin yanar gizo dubban dalolin kudi.
“Bayan samun wannan bayanan, an tura kwararru masu binciken laifuka ta yanar gizo da kadarorin sirri a karkashin kulawar DCP Uche Ifeanyi Henry, daraktan NCCC, kan lamarin.
“Kokarin da rundunar ta yi ya kai ga kama wani George Gift Ikata, wani matashi dan shekara 21 dan asalin karamar hukumar Abua a jihar Ribas. Wanda ke zaune a Iwofe, Jihar Ribas. Ya kirkiri shafin ne kawai don yin zamba ta yanar gizo.”