Wasu rahotanni na cewa, tattalin arzikin duniya zai samu tagomashi daga tafiye tafiyen yawon bude ido da Sinawa za su gudanar zuwa kasashen waje, a lokacin hutun ranar ‘yan kwadago ta bana, daya daga cikin lokutan hutu mafiya tsayi a kasar Sin.
A bana Sinawa masu tarin yawa sun shirya ziyartar wurare da dama, a karon farko bayan shafe shekaru 3 ana aiwatar da tsauraran matakan yaki a annobar COVID a cikin kasar, wanda hakan ya haifar da takaituwar tafiye tafiye. Kaza lika bikin na bana, na gudana ne tun daga ranar 29 ga watan Afirilu zuwa 3 ga watan Mayun nan. Shi ne kuma biki mafi tsayi na farko da ake yi a kasar, tun bayan sake bude zirga zirga ta rukunonin masu fita yawon shakatawa daga kasar a watan Fabarairun da ya gabata.
A cewar hukumar lura da harkokin yawan shakatawa ta MDD, Sinawa masu yawon bude ido ne ke kan gaba a duniya, wajen bunkasa kasuwar kasa da kasa a fannin, inda yayin tafiye-tafiye da suka gudanar zuwa ketare, tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019, suka kashe kimanin dalar Amurka biliyan 260 a kowace shekara.
Alkaluman shahararren kamfanin samar da hidimomin tafiye tafiye na kasar Sin Ctrip, sun nuna adadin masu duba tikitin jiragen sama a wannan lokaci ya karu da ninki 9, sama da na makamancin lokaci na bara, kuma masu neman hidimomin tafiye-tafiye zuwa ketare sun karu da ninki 18.
Har ila yau, wani rahoto daga kamfanin tantance alkaluma game da harkokin kasuwanni da cinikayya na Euromonitor International, ya nuna cewa, karuwar adadin masu tafiye tafiyen na wannan karo, ya zo a gabar da hada hadar sayayya ke kara fadada a kasar Sin.
Rahoton ya ce bisa matsakaicin hasashe, Sinawa masu fita yawon bude ido na kashe kudaden da suka ninka na shekarar 2019 har sau biyu. Ana hasashen Sinawa masu tafiya yawon shakatawa za su zamo a sahun gaba, a fannin samar da kudaden shiga, ga kantuna marasa dora haraji kan hajojin su, a jimillar fannoni 6 cikin 10 na kasuwanni mafiya muhimmanci, matakin da zai samar da harajin sayayya da darajar sa za ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 117. (Saminu Alhassan)