ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

MDD Ta Gudanar Da Bikin Ranar Tunawa Da Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Duniya Ta 2025

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Zaman lafiya

A ranar Laraba ne aka gudanar da bikin Tunawa da Ranar Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Duniya a ofishin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na Nijeriya. Babban bako a taron, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya Janar Christoper OFR. Inda a jawabinsa bayan maraba da baki ya ce, “Tunawa da Ranar Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta MDD Ta 2025, taro ne na tunatar da sadaukarwar da jarumanmu maza da mata suka yi wajen sadaukar da rayuwarsu don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.”

Ana aikin ne domin babu wata al’umma da za ta iya jure fuskantar tashe-tashen hankula a duniya, rikicin jin kai da karuwar rashin tsaro. Don haka dole ne mu ci gaba da yin aiki tare da yin magana da murya daya don samar da zaman lafiya, adalci da mutunci ga kowa. Dangane da haka, Rundunar Sojin Nijeriya ta ci gaba da dagewa wajen bin ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

  • Hadin Gwiwar Sin Da Yankin Turai Na Kara Kawo Haske Ga Tattalin Arzikin Duniya
  • Yadda Rashin Ɗaukar Wani Maniyyaci Ya Hana Jirgi Tafiya Har Sai Da Ya Dawo Ya Ɗauke Shi

Yana da kyau a lura cewa a matsayinta na mamba a Majalisar Dinkin Duniya, Nijeriya tun bayan samun ‘yancin ke ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen bayar da gudummawarta wajen wanzar da zaman lafiya da magance rikice-rikice a duniya. Bisa ga haka, sojojinmu sun yi aiki a karkashin tutar Majalisar Dinkin Duniya tare da girmamawa da ban mamaki a yankuna da dama na warware rikici a duniya.

ADVERTISEMENT

Hakika, Nijeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da ke kan gaba wajen bayar da gudunmowa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kuma jigo a kwamitin wanzar da zaman lafiya.

Wannan ba wai yana nuna karfin sojojinmu na fuskantar barazanar da ke tasowa bane kawai, har ma da nuna imaninmu cewa zaman lafiya a duniya nauyi ne na dukkan kasashe da masu ruwa da tsaki.”

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali. Nijeriya kuma na wakiltar ayyuka guda 8.”

Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace.

Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948, dakarun wanzar da zaman lafiya sun ceto mutum sama da miliyan biyu daga kasashe sama da 125 cikin ayyuka 71 da suka gudanar.

Tun da fari a jawabinsa na maraba, Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Kuma Mai Kula Da Ayyukan Jin Kai a Nijeriya Mohammed Malick Fall, maraba da zuwan bikin cika shekaru 77 na ayyukan samar da zaman lafiya na MDD ya yi, inda ya ce “Taro ne mai muhimmanci kuma ya zo daidai da cika shekaru 80 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya,” in ji shi.

“A tsawon tarihinta, Majalisar Dinkin Duniya babban aikinta ga al’ummar duniya shi ne inganta zaman lafiya, tsaro, ci gaba, da mutunta bil’adama, kuma ta yi fice a wajen cimma wadannan manufofi.”

“Tun daga 1948, Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido kan ayyukan wanzar da zaman lafiya fiye da 70, da ceton rayuka da dama da kuma yin aiki a matsayin mai magance manyan tashe-tashen hankula.

A halin yanzu, sama da dakaru 87,000 masu sanye da kaki ana tura su cikin ayyuka mabanbanta kamar 12 a duniya.

Wanzar da zaman lafiya ya kasance daya daga cikin abubuwan da Majalisar Dinkin Duniya ta fi gani da inganci.”

“Karni na 21 ya zo da qalubalen tsaro da ba a tava ganin irinsa ba kuma masu alaqa da juna. Wadannan suna bukatar sabbin hanyoyi, kakkarfan hadin gwiwa na yanki da na duniya, da kuma sake nazarin yadda muke gudanar da ayyukan zaman lafiya-musamman yayin da rarrabuwar kawuna na siyasa ke kara hana shawo kan lamarin.

Wannan shi ne dalilin da ya sa muka sanya wa taron ranar dakarun wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a yau, taken “Makomar wanzar da zaman lafiya,” kuma ya dace sosai, in ji shi.

MDD
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu

Ɗalibai Sun Rubuta Jarrabawar WAEC Cikin Dare A Duhu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.