A jiya Talata 2 ga watan nan ne aka gudanar da taron bazara, na kwamitin matakan ba da rangwame, da na hana samar da rangwame na kungiyar WTO a birnin Geneva. A yayin tawon, wakilin kasar Sin ya soki manufofi, da matakan ba da rangwame masu kunshe da nuna wariya da Amurka ke aiwatarwa, ya kuma yi kira ga WTO, da ta karfafa sa ido kan ayyukan Amurka da suka saba wa ka’idojin kungiyar.
Wakilin na kasar Sin, a cikin jawabinsa ya yi nuni da cewa, “Dokar rage hauhawar farashin kayayyaki” da Amurka ta kaddamar, ta yi amfani da dalilin kiyaye muhalli wajen ba da kariyar cinikayya. Kuma bisa hakikanin abubuwan dake cikin dokar, Amurka ta yi bayani game da “yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci” wadda ba ta dace da ka’ida ba, wanda hakan ya yi matukar lalata ka’idojin kasuwancin duniya.
Kaza lika kasar Sin ta yi kira ga Amurka, da ta soke matakan ba da rangwame mai tattare da nuna wariya da ba sa kan ka’idojin WTO, kuma kamata ya yi kungiyar WTO ta kara sanya ido kan ayyukan Amurka na take ka’idojinta, kana mambobin WTO su yi kokari tare, wajen kiyaye daidaito, da kare tsarin samar da sassan na’urorin laturoni na duniya, da na darajta hajoji. (Mai fassara: Bilkisu Xin)