Kankan da kai na Annabi (SAW) a bisa kololuwar matsayinsa da daukakar martabarsa da darajarsa, shi ne karshen Annabawa (mafi kololuwar daraja), shi ne cikakken Annabi sauran duk Na’aibansa ne, shi ne aka aiko zuwa ga duk halitta ya shiryar da halitta kuma ya yi nasara, har wadanda ba addininsa suke yi ba sun yarda ya yi nasara.
Sannan kuma kowa ya yarda ya yi Isra’i da Mi’iraji har sai da ya je ‘Kaba Kausaini’ sannan ya je fadar Allah amma duk da wannan babu wanda ya kai shi kankan da kai, ba shi da girman kai ko kadan. Abin da Allah ya ba shi babu wani da Allah ya ba shi kusa da haka. Sabida nauyin sirrin da ya dauka, kamar yadda Allah ya fada a Alkur’ani “inna sanulki alaika kaulan sakila”, (lallai za mu saukar maka da zance mai nauyi), Hausawa na cewa, bishiyar da ke da ‘ya’ya ta fi sun kuyar da kai, bishiya mai daga kai, holoko ce ba ta da ‘ya’ya.
Girman kai, ba shi ne sa kaya masu kyau ba ko zama a gida babba ko hawa abin hawa mai tsada ba. Wani daga cikin Sahabbai ya ce, Ya rasulallahi! Wallahi ni ina so a ce, rawanina ya fi na kowa kyau, rigata da takalmina sun fi na kowa kyau, Sai Annabi (SAW) ya ce masa, wannan ba shi ne girman kai ba. Girman kai, shi ne kin gaskiya da tauye hakkin mutane.
Ya ishe ka cewa, Annabi (SAW) ya fi kowa kankan da kai, an ba shi zabi tsakanin kasancewa, Annabi Sarki mai dukiya irin Annabi Dawuda da Sulaiman ko kuma Annabi Bawa irin Annabi Isah da Yahya, sai ya zabi ya zama Annabi Bawa, Sai Mala’ika Israfilu ya ce wa Annabi (SAW), ka yi bushara, sabida kankan da kai da ka yi, Allah ya zabe ka ka zama shugaban duk ‘ya’yan Adamu (AS) a ranar Alkiyama, kai ne farkon wanda kasa za ta tsage ma wa a ranar Alkiyama ya fito daga Kabari, kai ne farkon wanda zai yi ceto.
Sabida haka, ya dace Malamai da Shehunnai su gane, don ka zama Malami ko Shehi ba shi ne ka zama sarki ba, ka yi kankan da kai irin yadda Annabi (SAW) ya yi, sai Allah ya tara maka duk masu raunin da masu arzikin da masu mulkin duk a karkashinka.
An karbo Hadisi daga Abi Umamata yana cewa, wata rana Annabi (SAW) ya fito zuwa gare mu yana dogara Sanda, sai muka mike masa tsaye, sai ya ce mana don kankan da kai, kar ku tashi kamar yadda wadanda ba Larabawa ba suke mike wa shugabanninsu, shashinsu yana girmama Shashi, ni bawa ne, ina cin abinci kamar yadda bayi ke cin abinci, ina zama kamar yadda bawa yake zama.
Malamai suka ce, Annabi (SAW) ya fadi wannan ne don kankan da kai ko kuma sabida ba al’adar larabawa ba ce. Malamai suka ce, kar ka mike wa wanda bai da wani alkairi don girmamawa sai dai don tsoron sharrinsa, amma Sarki ko Shugaba ko Malami ko Mahaifi ko wani mai daraja, ka girmama shi da duk irin tsarin girmamawa na wannan al’ummar, sabida ranar yakin Khandaku da aka yaki bani Kuraizah, wadanda suka ce sun yarda da hukuncin Sa’adu bin Mu’azu wanda shi kuma an harbe shi a akan babbar jijiya mai rike da rai, Annabi (SAW) ya sa aka dauko shi a kan Jaki sabida ba ya iya yin komai, da aka kawo shi sai Annabi (SAW) ya ce musu “Kumu ila sayyidikum, ku mike wa shugabanku”. Ta wannan hadisi aka samu hukuncin mike wa shugaba.
Akwai wakoki da dama da Hassanu ya yi wa Sahabbai kan mike wa Annabi (SAW).
“In mike wa Shugaba dole ne a wurina, in ki mike wa wannann shugaban, sam banga ya dace ba a wurina.”
“Yanzu mai hankali mai fahimta zai ga wannan kyawun ya ki mikewa?”
Annabi (SAW) ya kasance yana hawa Jaki, yana yin goyo ma a kan jakin, yana zuwa ya gaida Talakawa, yana zama da Talakawa, yana amsa kiran bawa, in bawa ya shirya wata Liyafa, Annabi (SAW) yana amsa gayyata, yana zama tsakanin Sahabbansa a duk inda zama ya tike masa.
A cikin Hadisin Sayyadina Umar, Annabi (SAW) yana cewa, kar ku yi min yabo na kai karshe wanda zai janyo ku wulakanta wani Annabi. Yabon Annabi (SAW) na Shari’a yana nan, shi bawan Allah ne, saninsa kuma na Ma’arifa yana nan (Rasulun minallahi… Manzo ne daga Allah), “Ni haske ne daga Allah, Mu’uminai kuma haske ne daga haskena” duk wannan yabon yana nan. Karshe dai, Shari’a wurinta daban, Ma’arifa wurinta daban. Amma babu wani Arifi da ya yarda ka fadi abin da ka sani na Ma’arifa a wurin ‘yan shari’a, sabida hadisin Annabi (SAW) ga sayyadina Umar “Umar ka san ko ni waye?”
“Kar ku ketare iyaka wajen girmama ni kamar yadda Nasara ta tsallake iyaka” su ma Nasara in maganar Ma’arifa suke yi, su tsaya can. Imam Garzali ya yi littafi mai girma kan wadannan maganganu da ya sa Nasara ta tsallake iyaka a cikin littafinsa mai suna ‘Sarihul Injili’.
Annabi (SAW) a cikin kankan da kai, ya ce wa Sahabbansa, in za ku yabe ni, ku ce min “Abdullahi – Bawan Allah”. Sufaye suna cewa, wannan kuma shi ne daidai a ma’arifa, don karshen Arifi abinda zai tarar shi ne ‘Abdu’ “Subhanallazi asra bi abdihi lailan…– tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiya da bawansa da daddare…”
An karbo daga Anas cewa, wata mace, Ummu Zafarin (kila me yi wa Sayyada Khadijah kitso ce) tana da matsalar hankali kadan wani lokaci, ta zo ta ce wa Annabi SAW “ Ina da bukata a wurinka ya Muhammad” sai ya ce mata, “to zauna ya uwar wane (Annabi SAW ya yi mata alkunya, bai fada sunan danta ba ko kuma mai hadisin ya manta sunan dan da aka ambata), duk inda kike so in zauna in biya miki bukatunki a duk fadin garin Madina zan tsaya miki, ki zabi inda kike so mu zauna in ji bukatunki, ni kuma insha Allah zan yi miki duk bukatunki. Sannan ta zauna Annabi (SAW) shi ma ya zauna ta fada masa duk bukatunta. Manzon Allah (SAW) ya yi mata hakan ne a lokacin da Larabawa suke kin ‘ya’ya Mata.
Anas dan Malik ya ce, Annabi (SAW) yana hawa Jaki, yana amsa kiran Bawa in ya gayyace shi, ranar yakin bani Kuraizah, An ga Annabi (SAW) a kan jaki, an yi wa jakin linzami da ragama sannan jakin shimfida kawai aka yi masa.
Anas ya kara da cewa, ana gayyatar Annabi SAW zuwa walimar da za a ci gurasa da ake ci da kakiden da ya fara lalacewa sabida dadewa a ajiye. Malamai sabida wannan Hadisin suka yi fatawa, in mutane sun gayyaceka wurin taron al’adarsu suna da abinci mai wari, mara cutarwa kuma abincin mai girma ne a wurinsu, ba laifi kai ma ka hakura ka bi al’adar sabida girmamasu.
Anas ya ce, Annabi (SAW) ya yi aikin Hajji a kan wani tsohon sirdin rakumi, an sa masa wata ‘yar katifa, da katifar da sirdin gaba daya ba su kai Dirhami hudu ba, amma kuma Annabi (SAW) sai aka ji yana addu’a yana cewa, Allah kasanya wannan Hajjin karbabbiya wacce ba Riya a ciki.
Sabida kankan da kai na Annabi (SAW), a kan tsohon sirdin rakumi ya yi aikin Hajji amma a wannan zamani ga mu nan, a jirage na alfarma, a dakunan Hotel masu sanyi da alfarma muke yi.
Wanann shi ne Annabinmu (SAW), wanda aka bude wa arzikin da ke kan kasa baki daya amma ya hau sirdin rakumi tsoho. Hadiyyar rakuma 100 ya bayar aka yanka a wannan Hajjin.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa cikin yardar Allah