Kwamitin ayyuka na Jam’iyyar APC a matakin kasa (NWC) ya cimma matsayar zabar Sanata Godswill Akpabio daga shiyyar Kudu Maso Kudu a matsayin shugaban majalisar Dattawa da kuma Sanata Jubril Barau dan shiyyar Arewa Maso Yamma a matsayin mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta 10.
Sannan, jam’iyyar ta kuma zabi Hon. Hon. Tajudeen Abbas da ya fito daga shiyyar Arewa Maso Yamma a matsayin Kakakin Majalisar wakilai ta tarayya da kuma Hon. Benjamin Kalu daga shiyyar Kudu Maso Gabas a matsayin mataimakinsa.
Matsayar wacce jam’iyyar ta fitar ta wata sanarwar da sakataren watsa labaranta, Felix Morka, ya fitar bayan ganawar Majalisar Kolin jam’iyyar da ya gudana a shalkwatar APC da ke Abuja a ranar Litinin, domin yin nazari kan ganawar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da wasu kusoshi kwanakin baya.
Ganawar NWC ya yi la’akari da shawarori da ganawar da zababben shugaban kasan da wasu jagororin APC suka cimma dangane da batun rabon jagoroncin Majalisar dokoki ta 10 zuwa shiyya-shiyya na kasar nan.
Ganawar na NWC ya amince tare da mutunta matakin da Bola Ahmed Tinubu da masu ruwa da tsakin suka dauka, kana ganawar ya nemi a cigaba da tunuba da neman shawarorin sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an hada kan ‘yan takaran da suke Neman mukaman domin ganin an fahimci juna yadda ya kamata.
“Muna kira ga jagororin APC da mambobi da dukkanin ‘yan Nijeriya da su cigaba da yin aiki tukuru wajen kyautata zaman lafiya da cigaban kasar nan gabanin da bayan mika mulki.”