Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya gana da jakadan Amurka a kasar Sin Nicholas Burns, yau Litinin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar ta su, Qin Gang ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin Sin da Amurka tana da ma’ana matuka ga kasashen biyu, gami da duniya baki daya. Ya ce a halin yanzu ya dace a gudanar da huldar yadda ya kamata, yana mai cewa ya kamata ta kasance matsaya guda da sassan biyu suka cimma, don haka kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar martaba juna da zaman jituwa cikin lumana da hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, yayin da take daidaita huldar dake tsakaninta da Amurka, kamar dai yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Qin Gang ya kara da cewa, ya dace Amurka ta kara fahimtar yanayin da kasar Sin ke ciki da sanin ya kamata, kuma dole ne ta martaba hakkokin kasar Sin, kana ta daina yunkurin gurgunta ‘yancin kai da tsaro da moriyar samun ci gaba na kasar, musamman ma a bangaren da ya shafi batun Taiwan.
Bugu da kari, Qin ya ce yana fatan jakada Burns zai kara yin la’akari tare da cudanya da al’ummar Sinawa, ta yadda zai taka rawa wajen inganta huldar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mai fassarawa: Jamila)