Jami’an tsaro a Jihar Anambra sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da cafke wasu ‘yan fashi da makami.
Wannan ci gaban ya biyo bayan aikin hadin gwiwa ne da ‘yansandan suka gudanar tare da ‘yan banga, a cewar sanarwar ranar Talata daga kakakin ‘yansandan Anambra, Ikenga Tobechukwu.
- Shirin APC Na Zabar Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Tada Kura
- ‘Yansanda Sun Kama Kauraye 72 Da Ake Zargi Da Kwacen Wayar Salula A Katsina
“Wadannan ayyukan hadin gwiwa sun samar da babban ci gaba mai kyau a ranar 7/5/2023 da misalin karfe 8:45 na dare. ‘Yansandan da ke sintiri a Usmusiome Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa sun kama wasu gungun mutane hudu da ke aiki a cikin wata mota kirar Lexus SUV da ba ta da rajista, inda suka kwato wasu bama-bamai guda biyu, bindiga kirar AK-47 daya, harsashi masu dangon 7.62, laya da sauran abubuwa a hannunsu,” in ji sanarwar.
“Jami’an a lokacin da suke artabu da ‘yan bindigar sun kashe biyu daga cikin ‘yan kungiyar, yayin da wasu biyu suka tsere. Tuni dai aka fara kokarin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka gudu.”
Ya kara da cewa, a wannan rana, jami’an ‘yansanda a Azu Ogbunike, a yankin karamar hukumar Oyi a jihar Kudu-maso-Gabas, sun cafke wasu ‘yan fashi da makami guda hudu a yayin da suke lalata wata babbar mota da ake zargin ta sata ce.
“Dukkansu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa kuma a halin yanzu suna taimaka wa ‘yansanda da bayanai kan wasu ‘yan kungiyar da suka kwace motocin mutane da ba su ji ba su gani ba, kafin su kai su maboyarsu da ke Azu Ogbunike,” in ji kakakin.