Rahotanni na cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana a kwanakin baya cewa, kasar Sin ta dauki matakin tattara kwayoyin halitta na DNA na mutane ‘yan kananan kabilu dake jihar Xinjiang da yankin Tibet don sa musu ido.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, maganar Blinken ba ta da tushe, kawai ya tsara labarai ne da babu ma’ana ko kadan.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce dake bin dokoki, kuma tana tabbatar da hakkin dukkan al’ummar kasar daga kabilu daban daban bisa doka. Ya ce Amurka ce kasar dake tattarawa tare da yin amfani da kwayoyin halitta. Bisa labarin da jaridar The Wall Street Journal ta bayar, an ce, ma’aikatar tsaron Amurka ta riga ta tsara shirin yaki da abokan gaba ta hanyar makamai masu amfani da kwayoyin halitta.
Mahalartar shirin sun bayyana cewa, an shigar da kwayoyin halitta na Sinawan Asiya, da Aryans na Turai, da Larabawa na yankin gabas ta tsakiya a cikin shirin. Kowa ya san wanda ke amfani da kwayar halitta wajen aiwatar da ayyuka cikin sirri. (Zainab)