A Nijeriya, ana gudanar da zabukkan kasa ne kamar wata 3 kafin karewar wa’adin gwamnati mai barin gado, idan gwamnatin da take a kan karagar mulki ce ta lashe zabe ba a cika samun wata matsala ko takaddama a kan yadda za karbi mulki ba ko kuma a samu wasu korafe-korafe a kan yadda gwamnati mai barin gadon ke gudanar da ayyuka a cikin watanni ko kwanakin karshe wa’adinta.
Irin wadanna ayyuka da suke yawan kawo cece-kuce sun hada da kaddamar tare da fara sabbin ayyuka, kara wa ma’aikata girma, daukan ma’aikata aiki da kuma daukar sabbin manyan sakatarorin gwamnati, a wasu lokutta kuma ana samun gwamnati mai barin gado da kirikiro da wasu kananan hukumomi ko gundumomin raya kasa da sabbin masarautu.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Samfurin Tianzhou-6
- Yadda Hadin Gwiwa A Fannin Kiwon Lafiya Ke Amfanar Da Al’ummar Rwanda
Wadannan ayyuka suna bukatar kudade masu dimbin yawa wajen tafi da su, abin da kuma yana iya jefa gwamnati mai kamawa cikin matsalolin kudade, wanda hakan na iya sa a fada rikice-rikicen da zai iya hana sabuwar gwamnati farawa da kafar dama. A wasu lokutta gwamnati mai barin gado kan kusanci bankuna domin ciwo basuka wanda nauyin biyan su ke komawa kan gwamnati mai kamawa.
Gwamati mai barin gado kan dogara da cewa, ai wa’adin mulkinsu yana kaiwa ne har zuwa daren ranar da za a rantsar da sabuwar gwamnati, saboda haka suna da hakkin su ci gaba da gudanar da aikinsu a matsayin halattaciyyar gwamnati, duk da cewa, za su iya dogaro da doka a wannan matsayar amma a zahiri masana sun nuna rashin dacewar haka saboda kirkiro da wasu ayyukan da suka yi zai iya durkusar da gwamnati mai kamawa saboda matsalolin kudi, wasu kuma na ganin kamar tarko ne gwamnati mai barin gado ke dana wa mai kamawa don kada ta samu nasara.
Ana ganin cewa, tunda yawancin manufofin jam’iyyu ba daya ba ne, irn wadannan ayuyuka da ake yi a karashen wa’adin gwamnati mai barin gado na haifar da tsaiko ga gwamnati mai kamawa don za ta bata muhimmanan lokaci wajen zaman yin nazari tare da kokarin warware takaddamar da sabbin nade-naden ya haifar a tsakanin al’umma maimakon gwamnatin ta mayar da hankalin kai-tsaye wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma.
Ire-ren wadanna matsalolin sun bayyana a daidai wannan lokacin da ake shirin mika ragamar mulki ga sabbin gwamnatoci a wasu jihohin da ‘yan adawa suka lashe zabukkan da aka gudanar a Nijeriya, a ranar 29 ga watan Mayu 2023 kamar yadda tsarin mulki Nijeriya ya tanada.
Tuni jihohi irin su Kano, Zamfara Sakkwato, Filato da Benuwai, takaddama ta barke a tsakanin gwamati mai barin gado da kuma ta jam’iyyun adawa mai shirin karbar mulki. A Jihar Kano, gwamna ma jiran gado, Injiniya Abba Kabiri Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida na jam’iyyar NNPP ya nuna aniyarsaa da dakatar da wasu ayyyukan da gwamnatin Ganduje mai barin gado ta yi a karshe-karshenta da kuma wasu nade-nade da ya yi na sarakunan gargajiya a Jihar, wanda tuni a yanzu ake ganin za a samu takun saka. Labarin daya ne a sauran jihohi kamar su Zamfara, Sakkwato, Benuwai.
- Halin Da Ke Ciki A Jihohin Zamfara, Benuwai, Abiya Filato Da Sakkwato
A lokacin da ranar 29 ga watan Mayu, wadda za a gudanar da bukukuwan mika ragamar mulki ga zababbun gwamnoni masu wa’adi na biyu da sabbin masu kamawa daga bangaren adawa, sa-toka-sa-katsin da musayar zazzafan kalamai sun kunno kai, kan yadda suka yi tasarrufin kudaden jihohin, aiwatar da wasu muhimman ayyuka, al’amarin da yake nema ya zama tarnaki ga sabbin gwamnonin.
A jihohi 28 da hukumar INEC ta gudanar da zaben gwamna a ciki, jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasarar lashe jihohi 16; yayin da jam’iyyar PDP ta samu nasara a jihohi 10, jam’iyyar NNPP daya ita ma jam’iyyar Labour Party (LP) daya. Wanda kafin babban zaben, APC ta na da iko da jihohi 18 a tsakanin jihohi 28, inda PDP take da 10.
Har ila yau, jam’iyyu masu mulki sun sha kasa a jihohin Kano, Sokoto, Benuwe, Abiy, Filato, da Zamfara. Inda PDP ta sha kaye a jihohin Abiya, Benuwe, da Sakkwato yayin da ita ma APC ta yi faduwar bakar tasa a Filato, Zamfara, da Kano.
Jam’iyyar Labour Party (LP) ta kwace Abiya kana jam’iyyar Sanata Rabiu Kwankwaso, NNPP ta karbe Kano.
A cikin wadannan jihohin, zababbun gwamnonin sun baza na mujiya kan makudan kudaden da ake ciwo bashi, zargin almubazzarancin biliyoyin kudin gudanar da manyan ayyuka da wadanda za su gada ke yi.
Irin yadda gwamnoni masu barin gado suka yi kaurin suna wajen rashin yin kazar-kazar da tabuka abin a zo a gani a a wa’adin mulkinsu na tsawon shekara 8, sabatta-juyattan da ke gudana a jihohin Abiya da Benuwe, ya zama ‘yar manuniya kan irin yadda kurar ke ci gaba da tashi, dangane da yadda gwamnonin masu barin gado ke tafiyar da al’amurran wadannan jihohin, ta fannin tasarrufi da kudaden jiha, da kwangilar ayyuka ba bisa ka’ida ba, tare da daukar sabbin matakai a irin wannan kurarren lokaci kafin su bar ofis din.
Bugu da kari, zababbun gwamnonin sun bayyana fargaba dangane da halayyar wasu daga cikin gwamnonin ke nunawa, tare da yunkurin yi wa Baitil-malin jihohin kwab daya.
A jihar Abiya, Mista Aled Otti na jam’iyyar Labour Party (LP) ya daura zarensa a hannu, tsakaninsa da Gwamna Okezie Ikpeazu mai barin gado na jam’iyyar PDP. Yayin da a jihar Benue, musayan yawu ne ya kaure tsakanin zababben Gwamna a jam’iyyar APC, Reb. Hyacinth Alia da Gwamna mai barin gado, Samuel Ortom na jam’iyyar PDP.
Har ila yau, tsakanin Gwamna Lalong na jam’iyyar APC da zababben sabon Gwamnan jihar, Mista Mutfwang, na Filato wanda tuni ya karkade tabaransa, don samun damar keta hazon hango abubuwan da ke wakana daga nesa, ana kallon tarihi ne ke shirin maimata kansa a jihar.
Nasarar da Mista Mutfwang ya samu, al’amarin da al’ummar jihar Filato suka yi ta murna, za a iya cewa ba haka abin yake ba a zuciyar Gwamna Lalong. Mista Mutfwang shi ne tsohon shugaban Karamar Hukumar Mangu, bayan kimanin shekara daya da wata uku, Gwamna Lalong ya karbe mulki a hannunsa a sakamakon rusa shugabanin kananan hukumomin jihar a 2015.
A Jihar Zamfara, tun kafin lokacin zaben, rikici ya barke tsakanin manyan ‘yan takarar jihar; inda jam’iyyar PDP ta zargi Gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC wajen amfani da ‘yan daba su kai wa dan takarar Gwamnan jihar, Dr. Dauda Lawal hari.
Sannan bayan sanar da sakamakon zaben gwamnoni ke da wuya, Gwamna Bello Matawalle ya fito sarari tare da bayyana zargin cewa an yi amfani da sojoji wajen kwace masa mulki a jihar. Haka zalika, Matawalle ya ce kin amincewa da sabbin kudin da gwamnatin tarayya ta bullo dashi ne ya jawo masa.
Ana Zare Wa Juna Ido Jihar Kano
A Jihar Kano, da ake kallon lamarin kamar ya fi zafi, saboda tsakanin Jam’iyya mai mulki da mai jiran gado akwai adawa mai zafin gaske, musamman kasancewar ita Jam’iyyar NNPP na karkashin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda daman shi ne uban gidan Gwamna Ganduje mai barin Gado, abubuwa sun fara bayyana tuntuni.
Idan ba a manta ba, an samu adawa mai tsanani tun kafin Sanata Kwankwaso ya amince da tsayar da mataimakinsa Dakta Abdullahi Umar Ganduje takara a 2015. Wannan adawa ce ta yi tasiri inda shi ma Ganduje bayan samun damar darewa kan karagar mulkin Kano ya zare takobin ramuwar gayya ga tsohon uban gidansa ta hanyar yin wasu kalamai masu kama da jirwaye mai kamar wanka.
Tarihi ba zai manta da salon siyasar Jihar Kano ba domin irin wannan adawar asali ta samo tun a jamhuriyya ta biyu lokacin da Marigayi Gwamnan Jihar Kano Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi bayan kammala zangonsa na farko ya samu matsala da uban gidansa Malam Aminu Kano inda ya bar Jam’iyyar PRP ya kafa sabuwar Jam’iyyar NPP mai lakabin Canji, inda shi kuma Marigayi Sabo Bakin Zuwo Jam’iyyar PRP ta tsayar da shi a matsayin wanda ya yi mata takara kuma ya samu nasarar kayar da gwamna mai ci, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi a shekara ta 1983. Su ma a wancan lokacin an samu matsananciyar adawa tun Sabuwar Gwamnatin ba ta ci talata da laraba ba sojoji suka hambarar da ita.
Bayan dawowar demokuaradiyya a shekara ta 1999 Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso karkashin tutar Jam’iyyar PDP ne ya samu nasara kan jam’iyyar ANPP wanda ya samu nasarar mulkar Kano tsawon shekara hudu, a kakar zaben shekara ta 2003 ne tsohon Gwamna Kwankwaso ya sha kashi a hannun Malamin makarantar Malam Ibrahim Shekarau, wanda tun kafin zaben sakamakon alakar Malam Ibraahim Shekarau da harkokin addinin Musulunci yasa Kwankwaso sauke shi daga mukamin babban sakataren a kunshin Gwamnatin Jihar Kano ya mayar dashi malamin makaranta a makarantar share fagen shiga Jami’a (CAS). Duk da wannan nunawa malamin makarantar tsananin kiyayya Allah cikin ikonsa sai gashin shi ne dai ya rangada Gwamna mai ci a wancan lokacin da kasa, wanda alokacin mika mulkin aka dinga muzurai ana zarewa juna ido. A takaice dai haka Jihar Kano tayi ta fama da irin wannan sabata juyetan har zuwa wannan lokaci da ake shirin mika mulki daga Gwamnati mai ci wadda jam’iyyar adawa ta kayar a zaben shekara ta 2023.
Yanzu da ya rage ‘yan kwanaki a mika mulki ga subuwar Gwamnati, a Jihar Kano tuni kowane bangare ya kafa kwamitin karbar mulki domin tantance abubuwan dake kasa, a bangaren Gwamnati mai barin gado Ganduje ya nada Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji a matsayin shugaban kwamitin mika mulkin ya yinda ita kuma Jam’iyya mai jiran gado ta kafa nata kwamitin karkashin tsohon shugagabn hukumar TETFUND Dakta Baffa Abdullahi Bichi. Wani abinda dake nuni matukar adawa. Jam’iyya NNPP ta shigar da sama da mutane 700 cikin kwamitocin karbar mulkin, domin kowacce ma’aikata sabuwar Gwamnati ta kafa kwamitin da zai duba kunshin abubuwan da za’a mika masu.
Babban kalubalen da jama’a ke hange zai faru shi ne yadda gwamnatocin biyu ke adawa da junansu kan wasu muhaimman abubuwa da suke daukar hankalin Kanawa, musamman batun rushe-rushe da Gwamnatin NNPP ke ikararin aiwatarwa da zarar sun karbi mulki, kasancewar anji daga bakin jagoran Kwankwasiyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na ikirarin cewa koda da gini yakai tsawon hawa 100 matukar basu gamsu dashi ba sunansa rusasshe, harma akan jishi a unguwar koki yana tsinewa wani mutum da aka ce ya yi gini a hanya, sai kuma batun masarautu wanda shima anji Kwankwaso na cewa sabuwar Gwamnatin zata sake nazarin yadda aka tsige tsohon sarki Muhammadu Sanusi II wanda shakikin Kwankwaso ne, kuma idan haka ta kasance kenan sauran sabbin masarautun da Gwamnatin Ganduje ta kirkira zasu gamu da fushin sabuwar Gwamnati.
Akwai batun filayen da Gwamnati mai barin gado ta raba musamman a makarantu, masallatai, makabartu da Ganuwar Kano, suma wadanda suka mallaki wadannan wurare na cikin fargabar gamuwa da fushin Sabuwar Gwamnati. Domin ga duk wanda yasan halayyar Kwankwaso yasan mutum ne mai kafiya kan duk wani lamari da ya sa a gabansa, rushe gine ginen filin kofar Na’isa a lokacin zangonsa na biyu shaida ne kan irin yadda yake kokarin aiwatar da duk wani lamari da bai yi masa ba a tsarinsa.
Cikin abubuwan da ake ganin na iya zamewa Gwamnati mai barin gado barazana shi ne yadda tun kafin rantsar da Gwamnatin akaji Sabon Gwamna na jan kunnen Gwamnati mai barin gado kan dakatar da raba filaye, karbar basuka da daukar sabbin ma’aikata, domin tabbatar da wannan aniya ta sabuwar Gwamnati, jagoran darikar ta Kwankwasiyya an ji yana bayyana kansa a matsayin mashawarci na musamman ga sabon Gwamnan wanda kuma daman uban gidan sabon Gwamnan ne, hakan ke nuna cewa lallai da wuya ya bayar da shawarar da Abba Kabir Yusif zai yi watsi da ita. Hakan kuma yasa Wasu k e gsnin kamar ba Abba Kabir ne Gwamna ba, shi kawai umarni zai ci gaba da karba wanda hakan kuma ake kallo kamar ungulu ce da kan zabo ake shirin aiwatarwa a Kano
Wadannan dama sauran batutuwa sune a halin yanzu ke kara bayyana dumamar yanayin siyasar Jihar Kano, Jihar da ke zaman wata fitila a tarihin siyasar kasarnan, sai kuma yadda zawarawa kejeru daban daban ke kara baje kolinsu tare da ci gaba da kamun kafa ga mutanen da ake ganin suna da uwa gindin murhun sabuwar Gwamnatin.
Duk da irin wannan sabata juyetan har yanzu fa ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare, domin maganar da ake a halin yanzu Gwamnati mai ci yanzu ta jam’iyyar APC tuni sun garzaya kotu domin kalubalantar Nasarar Jam’iyyar NNPP, Wadda kuma kamar yadda bangaren masu kara ke kara hakurkurtar da magoya bayan Jam’iyyar ta APC cewa kowa ya kwantar da hankalinsa, domin a cewarsu sun tattara dukkan hujjojin da ake bukata domin kwace wannan nasara ta Jam’iyya NNPP, Musamman batun aringizon kuri’u da Jam’iyyar APC ke zargin jam’iyyar NNPP da yi tare da hadin guiwar wasu manyan mutane a kasarnan, sai kuma zargin da Jam’iyyar APC tayi cewa babu suanan Abba Kabir Yusif Na Jam’iyyar NNPP cikin kunshin sunayen da aka mikawa hukumar zabe mai zaman kanta na zaben fidda gwani.
Don haka lallai akwai tirka tirka da lokacin ne kadai zai iya ware tsaba da tsakuwa, yayin da suma magoya baya ake ta daure wasu da igiyar zato ta hanyar ko dai su bangaren jam’iyya APC suna ganin hujjojinsu sun kai makura da za’a iya ambata dan takarar jam’iyyar a matsayin wanda ya lashe zaben, ya yinda su kuma bangaren NNPP suke kara kwantar da hankulan magoya bayansu da cewa, sune suka kwace Santoci biyu daga cikin ukun da ake dasu a JIhar Kano, suka kwace sama darabin ‘yan Majalisar wakilai ta tarayya tare da kwace ‘yan majalisar dokokin jihar Kano sama da rabi, wannan a cewarsu wanda ya samu wannan gagarumar nasara shi ake kuma cewa za’a kwacewa nasarar sa?
Yanzu haka dai kamar yadda muka ambata sama kwanakin kadan suka rage ayi bikin mika mulki ga sabuwar Gwamnaaati, amma kuma sai akaji jagoran Gwamnati mai ci a yanzu Dakta Abdullahi Umar Ganduje na bayyana cewa zuwa yanzu shi bai ma san wanda zai mikawa Mulki ba, wannan kuma baya rasa nasaba da kyakkyawan fatan da su jam’iyyar APC ke yi a kotu.
Duk Da Adawar Siyasa, Akwai Fahimtar Juna A Jihar Sakkwato
Jihar Sakkwato ta na daya daga cikin jihohin da zaben su ya dauki hankalin jama’ar ciki da wajen kasa musamman a bisa ga yadda Jihar ke a karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal, shugaban kwamitin yekuwar neman zaben dan takarar shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar wanda kuma shine shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya.
Jam’iyyar APC a Jihar wadda Tambuwal ya yi galaba kan ta a zaben 2019 wanda ya bashi damar hawa wa’adin mulki a zango na biyu wanda ya kammala a yanzu, ta baiwa jama’a mamaki a yayin da dan takarar ta Ahmad Aliyu, tsohon Mataimakin Gwamna Tambuwal kana babban na hannun daman jagoran APC a Jihar, Sanata Aliyu Wamakko ya yi wa dan takarar PDP, Sa’idu Umar zarra a zaben.
Gwamna Tambuwal tuni ya ayyana sunayen manbobiin kwamitin da zai jagoranci hannun ta mulki ga sabuwar Gwamnati a ranar 29 ga Mayu. Mataimakinsa Hon. Manir Muhammad Dan’iya ne shugaban kwamitin mai manbobi 28 wanda aka dorawa alhakin hada hannu da Gwamnati mai jiran gado domin hannun ta mulki yadda ya kamata.
Bugu da kari jam’iyyar APC ta kaddamar da kwamitin mutane 108 da zai karbi mulki a hannun Gwamnatin Tambuwal. Jakada Abubakar Sani (Makaman Sakkwato) ne shugaban kwamitin wanda zababben Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kafa. Daga bisani shugaban ya kaddamar da kananan kwamitoci 18 da za su taimakawa babban kwamitin sauke nauyin da aka dora masa.
Masu fashin bakin lamurran siyasa a Jihar na ganin akwai dambarwa da kallo sosai a tsakanin jam’iyun biyu a tsohuwa da sabuwar Gwamnati musamman a bisa ga zazzafar adawar da ke tsakaninsu ta yadda ake ganin yana da wahala sabuwar Gwamnatin APC ba ta binciki Gwamnatin Tambuwal ba.
Gwamna Tambuwal mai barin gado duk da tsamin dangantaka da ke tsakaninsa da Tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Wamakko amma bai binciki Gwamnatinsa ba, bai kuma yi fito- na- fito da ita ba, hasalima bai fara aiwatar da nasa ayyukan ba sai da ya yi nisa wajen kammala kanana, matsakaita da manyan ayyukan da Wamakko ya assasa lamarin da ake ganin yana da wahala sabuwar Gwamnatin ta dauki irin tsari da salon siyasar Tambuwal wanda shi kansa ya bar manyan muhimman ayyukan da ba a kammala ba.
Al’ummar Jihar dai sun zuba idanu su gani a ranar hannun ta mulki, ko Tambuwal zai yi bayanin adadin bashin da ya gada a hannun Wamakko a 2015 da adadin bashin da ya biya na kudade da na kwangila da kuma adadin bashin da Gwamnatinsa ta karbo hawan ta mulki zuwa yau da kuma adadin bashin da ya biya domin bayyanannen lamari ne cewar idan ma ya ki cewa uffan, zai kasance babban abin mamaki idan sabuwar Gwamnatin Sakkwato ta yi shiru ba ta yi bayanin bashin da ta gada a hannun Tambuwal ba.
A yanzu haka shugaban jam’iyyar APC na Jihar, Isa Achida a makon jiya ya gargadi Tambuwal kan ya guji aikata abubuwan da ba su dace ba kafin bankwana da mulki. Ya ce sababbin mukaman da Gwamnatin Tambuwal ke yi da filayen da take rabawa a yanzu, duka za su yi bitar su.
Ya ce ba wai za su yi musayar kalamai da Gwamnatin Tambuwal ba, amma ba za su lamunci aikata abubuwan da ba bisa ka’ida ba da kuma gurbata tattalin arzikin Jiha. Ya ce Gwamnatin Tambuwal na da damar nada mukamai da bayar da filaye, amma su kuma APC suna da ‘yancin bita su gani idan an bi doka ko akasin ta.
Tuni dai dan takarar Gwamna na PDP Malam Sa’idu Umar da jam’iyyarsa suka shigar da karar zababben Gwamnan a kotun sauraren karar zabe a inda suke kalubalantar raba gardamar zaben wanda suke tababar sahihancinsa.