Rahotannin da ofishin kula da aikin harba ‘yan sama jannati zuwa sararin samaniya na kasar Sin ya gabatar sun nuna cewa, an harba rokar Long March-7 Y7 dauke da kumbon dakon kaya samfurin Tianzhou-6 a yammacin jiya Laraba 10 ga watan nan, da misalin karfe 9 da minti 22 bisa agogon Beijing, daga filin harba taurarin dan Adam dake Wenchang na lardin Hainan na kasar, kuma bayan mintuna goma, kumbon ya rabu da rokar, ya kuma shiga falakin da aka tsara.
Ya zuwa asubar yau Alhamis, da misalin karfe 5 da minti 16, kumbon ya hadu da sashen Tianhe, na cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, kuma daga baya sashen zai ci gaba da zirga-zirgarsa a sararin samaniya.
Aikin harba kumbon, shi ne na farko da aka gudanar, tun bayan da kasar Sin ta fara aikin amfani da cibiyar binciken sararin samaniyar ta, shi ne kuma aikin harba ‘yan sama jannati karo na 28 da kasar ta gudanar, haka kuma shi ne karo na 472 da aka yi amfani da rokokin Long March wajen harba kumbuna a kasar ta Sin. (Mai fassarawa: Jamila)