Humumar abinci da kula da harkokin noma ta duniya da ke a karkashin majalisar dinkin duniya (FAO), ta bayyana cewa, farashin kayan abinci a fadin duniya a watan Afilu ya tashi a karon farko a wannan shekarar.
Ta kuma sanar da cewa, farashin har yanzu na kan kashi 19.6 a cikin dari inda farashin ya karu a watan Maris na shekarar 2022.
- Manyan Jami’an Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Game Da Alakar Kasashen Biyu
- Yadda Likita Ya Yi Lalata Da Wata Mai Jinya A Asibitinsa A Jihar Kwara
A cikin rahoton tashin farashin da da hukumar ta FAO ta fitar na watan da ya wuce wanda kuma aka wallafa shi a ranar Juma’ar da ta gabata.
Rahoton ya nuna cewa, karuwar farashin a watan Afirlu ya faru ne kan kaya kamar su Nama, Shinkafa da Suga, inda kuma aka samu raguwar farashin kaya kamar su hatsi, Madara da Mai Gyada.
Rahoton ya ci gaba da cewa, an samu karin tashin farashin Suga ne saboda samun sauyin yanayi, inda hakan ya zama illa ga manyan kasashen da ke a cikin Asiya da suka kasance kan gaba wajen samar da Suga.
Hukumar ta FAO ta bayyana cewa, farashin Suga ya karu da kasha 17.6 a cikin dari daga watan Maris, inda farshin ya karu da yawa tun a watan Okutobar 2011.
A cewar hukumar, wannan ya faru ne saboda raguwar da aka samu na ragu a Indyia, China, Thailand da kuma a kungiyar turai wato EU, musamman saboda samun sauyin yanayio da kuma jinkirin da aka samu wajen girbe Raken da ake noma don sarrafa shi zuwa Suga, musamman a kasar Brazil
A bangaren Nama kuwa, rahoton ya sanar da cewa, farashin ya karu da kashi 1.3 a cikin dari, musamman saboda tashin farashin Kajin gidan gona, inda kuma aka sake samun karin bukatar ta Naman a da ake shigo da shi daga Asiya.
Har ila yau, farashin samfarin Naman na bobine na kasa da kasa, shi ma ya karu saboda raguwar da aka samu ta tura Shanun da ake yankawa, musamman a kasar Amurka.
Sai dai, farashin sauran kayan masarufi ban da Shinkafa ya ragu.
A bisa hasashen da hukumar ta yin na tashin farashin na kayan masarufin a daga shekarar 2023 zuwa shekarar 2024, ta yi nuni da cewa, akwai bukatar a a sanya ido a lokacin bazara a kasar ta Amurka.